Sunday, April 5, 2020

Garabasa: yadda zaku samu kyautan kudi sama da 1000 daga kamfanin palmpay
ABUBUWAN DA AKE BUKATA

 1. Waya kirar Android
 2. Sim card
 3. Palmpay app
 4. Natsuwa

Babu bata lokaci agurguje zan baku cikakken bayani akan Yadda zaku sami garabasar basai nai muku dogon bayani ba


Dafarko: kuje  ----> Play Store din wayar ku ka dauko Palmpay app

koku bi  link din kasannan ku dauko application din
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.transsnet.palmpay
bayan kun dauko saiku bude kuyi - Register, ku cike duk abinda suka tambaye ku a wurin invite code ku saka wayannan code din 6Q4609 Bayan kun kammala bude app din saikau dawo ku shiga wannan link din na farko -->  https://h5.palmpay.app/#/activity/lucky-money/binding/3820040121145647559742334/1585775696476


Bayan Ya bude zai baku wani form da zaku cike ku saka phone number/ da wannan security Question din
Saiku taba ----> Get Codes daga nan zasu turo da codes ta SMS saiku saka kuyi…Submit


Daga nan zasui maku Congratulations

Shima ka cikesa kamar Yadda kayi na farkon again zasui maku  Congratulations
Kawai saiku fito ku shiga wannan Palmpay app dinda ku kai Register ku duba sama zaku ga alamar NotificationsSaiku taba zaku ga 2 messages saiku shiga kowanne duk wanda ku kashiga zaku ga -Open) saiku taba kowanne zasu baku kyautar kudi mai taken  (Lucky money) daga nan ku dawo "Dashboard na app" wato homepage na application din  zaku ga Buy Airtime saiku shiga ku cire kudin ku 

YADDA ZAKU TARA KIMANIN 1000 DUBU DAYA A HAKA

Sannan zaku iya Accumulate ta Yadda zaku ta tara kudin

Da farko ku samu wayar abokanku  ko ma wace irin waya amman ta kasance android xe  saiku  tura app din ku bude kuyi register
Bayan kun kammala Register saiku dawo ku shiga wadancen link guda biyu dana baku a sama kuyi masa kamar Yadda ku kayi a naku na farkon

Sai ku sake shiga app din na wayar da kuke yin  kuje kuyi Open na Luck money
bayan sun bada kudin wajen cirewa ku saka number ku  kucire ahl haka zakui ta tarawa ko kuma ku shiga
Play Store ku dauko: Super Clone app- kaiyi ta Clone na apps din kana tara kudin....

Repost from Mr bazazzage

Thursday, April 2, 2020

Bayani akan USSD CODE na bankunan Nigeria da sunayensu
Assalam ayau zamu duba gefen bankunan Nigeria gaba daya, inda zamuyi bayani akan USSD CODE nasu da amfanin shi.

Hanyoyin Ajiya da ciran kudi a banki a Nigeria ya zamto mai saukin sauƙaƙawa a yanzu duk a ta dalilin USSD CODE.Kowanne banki da kuka sani  a Nigeria nada USSD CODE ko ince bank transfer code hakanan kuma duk wanda ya bude account da banki yana da daman yin amfani USSD CODE na bankinsa 

In kana amfani da UBA bank, hakan na nufin kana da cikakkiyar damar amfani da USSD CODE na su don saukake tura kudi zuwa wani account din ta hanyar wayarka

Koda saving account ne ka bude ko current account kana da cikakkiyar damar amfani da USSD CODE na bankinka  don saukake tura kudi ta hanyar amfani da wayar salula

Zamu lissafo maku Bank transfer code (USSD CODE) na kowanne banki dake Nigeria a nan kasa ammana kafin nan bari mu sanar daku ko menene USSD CODE da muhimmancinsa kana da amfaninsa

 Menene USSD CODE KO BANK TRANSFER CODE

bank transfer code wani tsari ne mai sauri da sauki kana mai tsatstsauran tsaro da zai baku damar sarrafa asusunku na banki cikin awanni 24 a rana guda, kana kwanaki bakwai 7 a mako guda ta hanyar amfani da wayoyinku batare da kun saka DATA ba, 

Kamar yadda kukaji nake ta fadin USSD CODE tsarine da aka fitar din saukaka hadadan banki, Wanda zaku iya amfani da da kowanne lokaci babu ruwansa da dare ko safiya ko karfe hudun dare ne zaku iya amfani da shi, hakanan batare da kunje banki ba kuna zaune a gidajenku cikin kwanciyar hankali kuna lallatsa wayoyinku zakuyi transfer din kudi zuwa wani account din batare da kunje kunbi sahun layi a banki ba don yin transfer ko makamancin sa, hakanan kowanne rana zaku iya amfani da shi babu ruwansa da ranakun hutu asabar da lahadi, sannan wani abun dadin ma shine baya amfani da internet bare azo ga batun cin data. 


AMFANIN USSD CODE

Da wannan USSD CODE din da muke magana akai zaku iya yin dukkan abubuwan da zan lissafo a nan kasa:

 • Zaku iya siyan kati (Recharge card) 
 • Zaku iya siya wa wasu ma katin (Recharge card)
 • Zaku iya duba kudadenku na banki (balance)
 • Zaku iya tura kudi zuwa wani asusun (transfer)
 • Zaku iya biyan bill (bill payment)
 • Zaku iya canza PIN na ATM card din ku 
 • Zaku iya siyan data
 • Zaku iya siyan ma wasu data
Ku fahimci cewa duka nan muna bayani ne akan USSD CODE, wani lokacin zaku iya ganinsa a USSD BANKING ko USSD MOBILE MONEY TRANSFER CODE dukkansu suna nufin abu guda ne 

So koda kunga wani abu makamancin hakan na gaba ina fata zaku gane cewa USSD CODE ne

JERIN USSD CODE NA GABADAYAN BANKUNAN NIGERIA

 1. UBA BANK code nasu *919#
 2. FCMB code nasu *329#
 3. ACCESS BANK code nasu *901#
 4. WEMA BANK code nasu *945#
 5. FIRST BANK code nasu *894#
 6. POLARI (skye) BANK code nasu *833#
 7. GTBANK code nasu *737#
 8. ZENITH BANK code nasu *966#
 9. ECO BANK code nasu *326#
 10. STANBIC IBTC BANK code nasu *909#
 11. DIAMOND ACCESS BANK code nasu *426#
 12. FIDELITY BANK code nasu *770#
 13. STERLIN BANK code nasu *822#
 14. UNITY BANK code nasu *7799#
 15. JAIZ BANK code nasu *389*301#
 16. KEYSTONE BANK code nasu *7111#

Friday, March 27, 2020

[tips] Yadda zaku saita kira kyauta da layin MTN 2020 new cheat
Assalamualaikum kamar yaddda kuke gani a title din a wannan darasi zaku koyi yadda zakuyi kira kyauta da layin MTN kudai kawai ku nutsu ku karanta darasin daga farko har karshe

Wannan Trick din zai baku damar yin Abubuwa kamar haka a layikanku:
 1. Zaku iya kiran ko wanne network dake Nigeria da shi
 2. Bakwa bukatar kati yayin yin kira wato kiran kyauta ne
 3. Kuna bukatar namba ta musamman wato Special Number yayin aiwatar da trick din
 4. Trick din baya karewa sannan babu kayyadadden lokacin da aka ɗiba masa na karewarsa a takaice dai MARAKAREWA NE
 5. A yanzu dai MTN basa sane da wannan trick din ammana a kowanne lokaci izan suka sani zasu iya kullewa


YADDA ZAKU YI

kubi matakan sa zan lissafo a kasa cikin takatsantsan in ba haka ba kuwa bazai yi aiki wa layinku ba

Sannan dole ku kasance masu hakuri yayin aiwatar da trick din


Wannan trick din yanayi da gaske don sai da muka tabbatar muka kuma tantance kafin mu kawo maku

Da fari kuje ku siyo sabon layin MTN wanda ya fara da ɗaya daga cikin nambobin ƙasannan:
 1. 081640***
 2. 081641***
 3. 081642***
 4. 081643***
 5. 090611***
 6. 070630***
 7. 080641***
Dole sai ya kasance nambar layinku ya fara da waƴannan prefix din kafin ku iya aiwatar da trick din 

So sai ku nutsu ku duba layin daya fara da ɗaya daga cikin nambobin dana lissafo a sama, bayan kun samu sai kuyi registan layin kamar yadda kuke registan kowanne layi


Sai ku sayi katin 100₦ ku saka layin sannan kuyi kira na ƴan mintoci sabida ku activating layin


Mataki na gaba kuje phone settings na wayarku ku shiga Mobile Network ku sake shigan Network Operators sai ku taba kan Select Manually.

Zaku  jira har network din su yi searching izan suka gama zasu baku lists din network din da suke available 

Zaku iya zaban kowanne network kuyi register da shi amman banda MTN
Zaku yi maku message akan baku zaba daidai ba kawai ku rabu dasu

Daga nan sai ku tafi izuwa dialpad naku ku kira nambar da kuke da bukatar kira amman kafin kuyi kiran sai ku ƙara nambar 9 guda uku agaban nambar da zaku kira din
Misali: izan kuna son ku kira wannan nambar 08123567689 sai ku saka kamar haka 99908123567689
Bayan kun kira zasu sanar da ku cewa "the number does not exist" wato babu makamancin nambar a kundin network din sai ku sake komawa wurin setting na wayarku kuje network ku sake zaban wani network Operator din amman kada ku zabi MTN

Sai ku sake komawa dialpad naku ku dialing nambar da kuke son kira kada ku manta ki saka 999 a farkon nambar da zaku kira sai ku kira izan baiyi ba sai ku sake canza Network operator ku dawo a haka zaku bi ku riga gwada network Operator din har sai kun samu wanda yayi ammana kada ku zabi MTN izan kun samu wanda yayi shi kenan sai ku more kiranku unlimited mara iyaka


Saturday, March 21, 2020

[tutorial] Yadda zakuyi welcomed back na layin Airtel da kanku cikin mintuna biyu 2
Nasan zaku kasance cikin mamaki da al'ajabin yadda nace zakuyiwa simcard naku na Airtel wellcomed back cikin abunda bai wuci mintuna biyar ba

Bayanai ne daki daki zanyi wanda muddin kuka bi bayanan nawa zaku kai ga ci,
Shin Airtel sim naka ko naki ya bace ko ya lalace kuma kuna da bukatar dawowa da shi don cigaba da amfani da layin tom sai ku girgije idanuwanku ku karance wannan darasi tsaf tun daga farko harya zuwa karshe, don sanin yadda zakuyi wellcomed back da kanku cikin mintuna biyar batate da kunje branch na Airtel ba kuma batare da kun kira customer care ba

Abun da kawai kuke da bukatar aikatawa shine tura sakon SMS ta hanyar bin bayanan da zanyi a nan kasa shi kenan bukatarku zata biya

ABUBUWAN DA AKE DA BUKATA

 1. wayar da zata iya tura sako SMS
 2. Sim pack din Sabon layin Airtel
 3. Sim pack din tsohon layin Airtel wanda zakaiwa welcome back

Bayan kun tabbata kuna da abubuwan dana lissafo a anan sama sai kuje wurin tura sakon SMS a wayarku ku rubuta:

SUNANKU (sai ku bada gab) NAMBAR WAYAR DA ZA'A SANAR DAKU IZAN YAYI (sai ku bada gab) NAMBAR WAYAR DA KUKE SON KUYIWA WELCOME BACK DIN (ku sake bada gab) SERIAL NUMBER NA TSOHON LAYIN (ku bada gab) SERIAL NUMBER NA SABON LAYINKU (ku sake bada gab) PUK NUMBER NA TSOHON LAYIN (ku bada gab) PUK NUMBER NA SABON LAYIN (ku bada gab) NAMBAR WAYAR SABON LAYIN DA KUKA SIYO
bayan kun gama rubutawa Alura da kyau wurinda kukaga na saka (ku bada gab) ina nufin ku bada space kada ku harhada rubutun sannan kada ku saki layi
PUK NUMBER da SERIAL NUMBER zaku samesu a jikin Sim pack na layinku.

 Bayan kun gama sai ku tura rubutun zuwa 190 , ku tabbatar da bakuyi kuskure ba, service din kyautane bazasu cajeku sisi ba, bayan kun tura Airtel zasu yi maku sauran aikin
Ga wayanda haryanzu basu gama fahimta ba to ga misali a nan kasa na yadda zasu rubuta sakon.

Shuraihu Usman 08022220000 07020000022 87390123400010003232 89235678900100400012 78765699 685455555 08021111122

Bayan kun tura zai dau sa'o'i 24 zuwa 48 kafin su bude maku layin 
Kutabbata da kun saka nambar da zasu tuntubeku izan suka kammala,
Ku more sassaukar welcomed back naku

Thursday, March 12, 2020

[tutorial] Yadda zaku bude adireshin GMAIL : bayani cikin hotuna
Gmail account abune mai matukar amfani a rayuwar wannan zamani domin kuwa kusan duk wani abu da zaka ga anayi zaka samu ana bukatan email address,

Kamar jamb,bude account na banki da dai sauransu, kafin mu tafi ga darasinmu gadan gadan zamu ɗan yi gajeran bayani akan muhimmancin Gmail dama amfaninsa

Da farko menene EMAIL

 A turance izan aka ce EMAIL a na nufin Hanyar aika sakonni daga wani wuri zuwa wani wuri ta hanyar amfani da na'ura ko ince lantarki

Dakwai kamfanoni da dama dake bada daman mallakar Email cikinsu kuwa akwai gmail,yahoomail,hotmail e.t.c 

In Allah ya yarda muddin kuna tare da mu duk zamu yi maku bayani dalla dalla akan yadda zaku bude Email da kamfanoni da muka lissafo a nan sama, amman bari mu fara da Gmail

Muhimmancin Email 

Kamar yadda na fada maku ne a sama cewa Email yana da matukar muhimmanci domin kuwa yanzu babu shafin da zakaje kayi register ko joining nasu batare da ka sanya email naka ba don su rika aiko maka da sakonni, 

Ku dau misali da JAMB, sanin kanku ne dole sai mutum yana da Email address sannan ake bude masa jamb, to amman kun taba yin tunanin dalilin ya sanya ake bukatar Email a Jamb, 

Babban dalilin daya sanya jamb ke bukatar Email naku shine don turo maku da sakonni, in baku manta ba na sanar daku Amfanin email dama kenan turo da aika sakonni ta internet, ta email naku jamb zasu na tura maku duk wasu informations daya danganci jamb account naku bama tare da kunje portal nasu ba

Kuna da sanin da cewa a facebook izan kuka sanya Email naku zasu rika turo maku da duk wani activities da kukayi a facebook ta Email inbox naku, a takaice dai Email kamar SMS yake ta wani fannin ma yafi SMS amfani dun shi international ne a kowacce kasa zaka iya amfani da ita sannan daga kowacce kasa za'a iya turo maki da sako ta cikinta kuma zaku iya turawa

Menene GMAIL

Gmail na nufin GOOGLE MAIL wato kamfanin aika sakonnin EMAIL na Google kusan a duk gabadayan kamfanonin Email na duniya mutane sunfi amfani da gmail, sannan koda ma ace mutum yana amfani da yahoomail ko hotmail kai kuma kana amfaninda gmail zaka iya tura masa sako babu damuwa

Yadda zaku bude account da gmail

Da fark kubi link dinnan 
https://accounts.google.com/signup/v2/webcreateaccount?flowName=GlifWebSignIn&flowEntry=SignUp
Zai kaiku wani wuri kamar haka

Sai ku cika form din 
A akwatin farko zaku sanya sunanku kamar yadda kukaga na saka

Akwati na biyu kuma sai ku sanya sunan babanku 

Akwati na uku kuma sai ku rubuta yanda kuke da bukatan adireshin gmail din ya kasance misali kamar shuraihu009@gmail.com

Akwati na hudu kuma wurin saka password ne (kalmar sirri)

Akwati na biyar zaku maimaita kalmar sirrin da kuka sanya a akwati na hudu don tabbatar da kun saka daidai

Daga nan sai ku danna maballin next zai kawoku wanni shafi makamancin hoton kasannan


Akwatin farko zaku sanya nambar wayarku

Akwati na biyu kuma zaku sanya Recovery Email Naku
Recovery Email: na nufin wani Email wanda yake naka ko na Abokinka, koda an samu akasi ka manta password din wannan email din naka zasu bukaci ka sanya Recovery Email din daka saka a anan  ko kuma izan ana kokarin ai maka hacking Gmail in mutum baisan Recovery Email naka ba dole yayi hakuri, 
Izan bakwada da wani Email din sai kubar wurin empty batare da kun saka komai ba

Abu nagaba shine Shekarun haihuwarku,
Da farko zaku saka watanni a karkashin akwatin month, sai ranan da aka haifekun a karkashin akwatin days shekarun kuma akarkashin years
Misali: 11 - 04 - 2000

Abu nagaba shine ku zabi jinsinku, 

Abun lura: kada kuyi gangancin saka shekarun karya wanda bana haihurwarku ba, domin kuwa a nan gaba zasu iya bukatar da ku dora government ID naku 

Bayan kun gama saita duk wannan sai ku danna nextA wannan shafin zasu bukaci ku sanya nambar wayarku izan kuka saka zasu turo muku da verification code ta SMS 
Sai kuyi minimize kuje inbox naku ku kwafe code din sa'annan ku dawo ku zuba shi a wurinda suka bukata


Daga nan zasu kawoku shafin samannan sai ku danna kan Yes I'm in

Zasu kawoku wurin dokokinsu kuyi kasa ku danna Agree Kai tsaye zasu kawo ku profile naku kaman haka


A nan zaku iya canza duk  wasu bayanan account din kama daga kan hoto,suna,ranar haihuwa da dai sauransu

Anan muka kawo karshen wannan darasi mun barku lafiya

Duk mai tambaya sai ya ajjiyeta a commentFriday, March 6, 2020

[tutorial] Yadda zaku duba Jamb Slim na 2020 ku printing nashi
A yau da safe Hukumar Jamb suka sakan ma duk wanda yayi register din jamb slim nashi dakwai hamyoyi biyu da zaku iya printing slim naku 
 1. Ta jamb portal
 2. Ta Email dinku

 1. Hanyar farko da zaku printing jamb slim naku na shekarar 2020 shine ta hanyar shiga portal din Jamb, Ku bi link dinnan https://www.jamb.org.ng/ExamSlipPrinting2/PrintExaminationSlip izan ya bude zai kaiku portal din jamb sai ku sanya Email ko Register Number ko Nambar wayan da kuka yi registan Jamb da shi, bayan kun saka sai ku danna maballin PRINT MY SLIM a nan take zai bude maku slim na jamb dinku mai dauke da Duk bayanan ku da gari gamida rana da lokacin  da zaku rubuta, Zaku iya saving page din a chrome browser sai ku kai cafe a printing maku
 2.  Hanya ta biyu shine ta Email din da kuka yi registan Jamb, Zaku ga sun Aiko maku da sako, ku bude sakon zaku tsinkayi File mai dauke da Slim naku sai ku downloading file din zai zo a document ba zaku iya bude shi ba sai da reader, amman izan kukaje cafe su sun yadda zasuyi su printing maku cikin sauki
Mun barku lafiya


Thursday, March 5, 2020

[free browsing trick] Sayi data 1.5GB akan 300 Naira da 75MB akan 20 NairaKwana biyunnan fa Kamfanin MTN faso gari da tsarukan sayen data masu rahusa wanda da yawan mutane basu san da su ba

Wannan tsari dai ana kiransa data offers 4ME 
Tsarin Data offers 4ME zai baku daman siyan data din da zamu lissafo a nan kasa


 1. 75MB akan 20 Naira

 2. yadda zaku siya


  kuje dialing pad na wayarku ku dialing *121# sai ku zabi data offers for me zai kawoku wurinda zaku ga jerin data din da zaku iya siya sai ku zabi na daya 1 daga nan zasu ciri 20 naira a balance naku su baku 75 MB tsarin nayi a kowanne layin MTN

 3. sayi 1.5GB akan 300

 4. Yadda zaku siya


  Shima wannan din dai zaku dialing*121# daga nan ku zabi Data Offers 4ME sai ku zabi namban 1.5 GB akan 300 anan take zasu baku 1.5GB sa'annan su zari 300 Naira a kudin lalilatarku (balance)

 5. sayi 4GB akan 1000

 6. Yadda zaku siya


  Kuje dialing din wayarku ku dialing *121# daga nan ku zabi Data Offers 4ME sai ku zabi namban 4GB akan 1000 anan take zasu baku 4GB sa'annan su zari 1000 Naira a kudin lalilatarku (balance)

 7. sayi 700MB akan 500

 8. Yadda zaku siya


  Shima wannan din dai zaku dialing*121# daga nan ku zabi Data Offers 4ME sai ku zabi namban 700MB akan 500 anan take zasu baku 700MB sa'annan su zari 500 Naira a balance naku

 9. sayi 1.5GB akan 500

 10. Yadda zaku siya


  Kuje dialing pad ku rubuta *121# daga nan ku zabi Data Offers 4ME sai ku zabi 1.5GB akan 500 anan take zasu baku 1.5GB sa'annan su zari 500 Naira a kudin lalilatarku (balance)

Sai dai fa ku sani data din nayin tsawon kwanaki 7 ne kacal sa'annan suyi expire

Tuesday, March 3, 2020

Hanya mai Sauki da zaku amshi Facebook account naku daga hannun hackers
Dandatse (hacking) wa mutane facebook account ya zama ruwan dare kusan kullum da ko yaushe  sai kun samu an dandatse facebook din wani, 

Wasu Mutane na tunanin ko daga facebook ne suke kulle masu account basusan cewa hackers bane ke hacking don biyan wata bukata ta su, 

Yanzu fa da anga kana da followers da friends 5000 kuma kana da friend request a kasa da suka kai 300 tofa ka shiga uku da hackers don sun rika kau ma account naka wafta kenan har sai sanda sukai nasarar wafce Account din a hannunka sannan zasu sami sukuni, 

Nasan mutane da dama zasuyi tunanin to wai ma su hackers dinnan ko da sun hacking account na mutane me suke da shi ko kuma me zasuyi da shi, wani Abokin a facebook ya taba yi min irin wannan tambaya, murmushi kawai nai masa nace da shi ai yanzu a kaf fadin facebook babu wanj abu mai daraja da ake siyansa da tsada kamar Facebook Account da Facebook page .

Abun dake faruwa shine aduk lokacin da aka kwamushe muku account sai a siyarwa wani ko wata ko shi wanda ya hacking din ya ruga amfani da account din,  dakwai darasi mai zuwa da zanyi maku bayanin Abunda ake da account din izan an siya 

Yanzu kam zamu fada kan darasinmu gadan gadan, 

Izan ya kasance ka samu kan ka daga cikin wayanda aka kwamushe musu Facebook Account,  kada ka dami kasha kuruminka kawai ka kwantar da hankalinka ka karanta wannan darasi namu a nutse

Dakwai hanyoyi da dama da ake kwamushe wa mutane Account sannan izan aka kwamushe maka account za a iya canja password din account din

IZAN AKA KWAMUSHE MUKU ACCOUNT KUMA AKA CANZA PASSWORD.

Yawancin hacking facebook account da hackers keyi suna yinsa ne ta hanyar canza password sabida kada mamallakin Account din ya samu damar shiga, balle ma har yayi da shi

Kwato irin wannan Account din daga hannun makwamusa wato hackers abune mai sauki,  wanda Alal hakika yafi komai sauki, kawai kubi wayannan matakai na kasa don dawo da account naku 

MATAKI NA FARKO
EMAIL & PHONE NUMBER

Izan ya kasance password ne kawai aka canza a account din kuma kun connecting Account din da Gmail Adress naku, sannan kuna da daman shiga Gmail din ko kuma Nambar da kuka bude account din yana wayarku 

Sai ku shiga facebook din kuje kan Forgot password , dake kasan facebook login page, 
zai kaiku wani shafin na daban inda zasu bukaci da ku sanya Username, ko Email Adress ,  ko Phone number, naku wanda kuka bude facebook din da shi, 

Bayan kun saka daya daga cikin ukunnan sai ku taba kan maballin continue 

Izan nambar waya kuka sanya zasu turomaku da recovery code ta layinku a SMS sai ku kwafo Recovery Code din ku dawo shafin ku zuba shi, 

Izan kuma Email adress kuka sanya shima zasu tura maku recovery code ta Email naku sai ku minimize kuje inbox na Email naku ku kwafo code din ku dawo facebook ku zuba shi

Bayan kun zuba sai ku taba maballin continue, anan ma zai sake kawoku izuwa wani shafin na daban wanda shi kuma zasu nuna maku inda zaku sanya sabon password,  izan kuka saka sai ku sake sanyawa a akwatin kasa wanda shine na confirm, 

Abun lura,  Yana da kyau yayin saka password ku saka password mai matukar wahala wanda ya hada da manyan Haruffa,ƙananan haruffa, symbol, nambobi, MISALI: E23e45&#s86@)ytech990@$_-;:
Daga nan Kai tsaye zai kai ku want shafi inda zasu nemi kuyi LOGOUT OF ALL SESSION, Ma'anan hakan kuwa shine zakuyi LOG OUT aduk wata waya ko kwamfutar da aka taba login Facebook account naku, na wayan da kake amfani da itace kawai bazatayi logout ba, bayan kunyi hakan zasu nuna maku Activities na account naku, Sai ku duba dakyau duk activities da kukasan baku yi ba Sai ku deleting na shi,

MATAKI NA BIYU

Idan kuma ya kasance bayan maƙwamushin ya ƙwamushe account din ya canza password, naka Sannan ya canza phone number naka, 
Kaga baka da daman yin aiki da matakin farko kenan sai de ka jarabawar mataki na biyu wanda yanzu sanyi bayani akansa,

Manyan maƙwamusa da suka ka san harkar sosai basa ƙwamushe Facebook account batare da sun canja Email,phone number da ma wasu abubuwan ba,

Idan ya kasance ka samu kanka cikin waƴanda aka ƙwamushe musu account kuma aka canja email da phone number to kasha kuruminka 

Kawai ku shiga facebook kuje login page wato shafin shiga, a kasan shafin zakuga forgot password, sai ku taba kansa zasu nuni maku wani Form sai ku saka sunan da kuke anfani da shi a facebook, zai danyi searching kafin ya nuni maku jerin mutane masu amfani da irin sunan da kuka saka sai ku duba hotonunansu zaku ga naku sai ku taba kan hotonku, 

Zasu kai ku wani shafi inda zasu bukaci su resetting password naku, sai ku taba kan “no longer have access to these” , 
Daga nan zasu baku Recovery Option wato sabon hanyar da zasu dawo maku da account, sai de tsarin ya dangata ne da adadin shekarun da ka diba kana facebook, idan account naka yakai akalla shekaru biyar zuwa sama a facebook to zasu baka security questions ne kawai wanda kana amsashi shikenan zasu bude maku account ku canja password

Idan kuma account naka sabone haifi shekara guda ba ko bai watanni uku zuwa hudu zasu baku tsarin "trusted contacts”
Sai ku zuba nambar email address naku da kuke amfani da shi sannan ku danna kan reveal my Trusted contacts,  sai ku sanya sunan daya daga cikin su,
Shin su waye Trusted contacts: trusted contact wasu daddaikun mutane ne da ake zabansu a matsayin Amintattun Mutane, wanda amfaninsu shine izan facebook account naka ya samu matsala ko aka hacking zasu taimake ka wurin dawo da account din , kuma dai kaine zaka zabi waƴannan mutane daga cikin Abokanka, wasu daga cikinku sun san yadda ake zaban mutum a matsayin Trusted contacts wasu kuwa basu sani ba to kada mu damu nan gaba kadan zanyi bayanin yadda zaka zabi wani a matsayin Trusted contacts dinka
Bayan kun saka sunan daya daga cikin Trusted contact naku facebook zasu tura masu da link sai ku bukaci su bude link din su dauko maku code din security code da suke nema, bayan sun fada maku sai ku saka code din a muhallin da shi kenan

MATAKI NA UKU 
Idan ya kasance maƙwamushin daya ƙwamushe maku account ya canza Email facebook zasu aiko maku da sako a tsohon email naku zasu sanar daku kokarin canza email din da ake yi a kasan sakon zakuga sun rubuta "if you did not do this, please secure your account" sai ku taba kan rubutun zasu kawo ku inda zaku tsaurara tsaron Account naku, 
Sannan zasu baku hanyoyin dawo da account nakun,

 HANYAR FARKO

Hanyar farko shine ku dora Katin shaidar gwamnati, wanda zai iya zama , katin zabe, voters card, national Id card Katin ɗan kasa, da dai sauransu duk dai ID card din Daya shafi gwamnati zaku iya dorawa
Bayan hakan facebook zasu bude maku account naku kana su baku daman canza password

HANYA TA BIYU

Hanya ta biyu itace facebook zasu bukaci ku sanya shekarun haihuwar ku, wata, da kuma rana, kamar dai yadda kuka sanya a profile naku izan dai wanda kuka saka yayi daidai Dana profile naku zasu bude maku account din kana su baku daman canza password

HANYA TA UKU

Hanya ta uku kuwa facebook zasu shiga profile naku su dauko hotunan Abokanka su rika nuna maku ɗaya bayan ɗaya, abinda suke bukata shine duk hoton da suka nuna maku to aka san hoton akwai Option Mai dauke da sunaye biyar zuwa shida, sai ku zabi sunan Aboki ko ƙawarku dake jikin hoton a cikin Option dinnan Wanda Kuma sunan yazo daidai dana hoton, izan kuka zabi sunayen Mutane biyar daidai shi kenan zasu bude maku account su nemi ku canja password.


Idan ya kasance kun gwada duk wa'yannan matakai da hanyoyin dana lissafo amma baku samu nasarar dawo da account naku ba tom akwai wasu sabbin hanyoyi da facebook suka fitar da su kwanan nan akan matsalar hacking wa mutane facebook account, ga sabbin hanyoyin a nan kasa.

SABUWAR HANYA TA ƊAYA

facebook sun fitar da sabuwar hanyar dawo da account din da maƙwamusa suka ƙwamushe ta hanya mai sauki wanda a wani lokacin ma ba sai kayi verification ba kawai abinda ake bukata shine kayi resetting password naka a cikin wayar da mafi shigar facebook da ita, wato wayar da akullum da ko yaushe kake shiga da ficen facebook da shi, misali;
Ka kai tashin shekara guda ko wata uku kana amfani da infinix smart 2, to Kuma rana tsaka sai aka ƙwamushe maka account, to muddin kana bukatar ka dawo da account naka cikin sauki sai ka shiga facebook ta infinix naka nan facebook zasu recognizing wayar taka, wato zasu gane ta tunda dama can da itace ka saba shiga, zasu tabbatar da kaine ba wani ba

Hakanan ma izan ya kasance mafi shiga facebook da wifi to sai kayi amfani da wannan wuri din da ka saba shiga da shi wurin resetting password din

SABUWAR HANYA TA  BIYU

kwanan nan facebook suka samar da wani tsari wai shi identity verification 
Da wannan tsarin zaku iya dawo da ƙwamusashshen account naku ta hanyar turawa facebook (government ID) wato shaidar tabbatarwa ta gwamnati kamar voters card, national ID card ,driven license da dai sauransu bayan kun tura facebook zasu duba bukatar ku na tsawon kwana ɗaya zuwa kwana uku sannan su taimakeku wurin dawo da account naku daka ƙwamushen cikin sauki, muddin kuka bi wa'yannan matakai na kasa

Ga matakan da zalunci wurin tura masu da Government ID naku:
Zai kaiku wani shafi sai ku cike dukkan Form din da suka bukata sannan ku dora government ID naku, 
Bayan kun cike sai ku tura Form din zuwa facebook ku tsumayesu na ɗan kwanaki
Daga nan facebook zasu turo maku da sakon Email mai dauke da likau (link) din da zaku bi ku dawo da account na ku sannan ku canza password

Waƴannan hanyoyi da matakan da mukai bayani akan su sune hanyoyin da zaku bi wurin dawo da facebook account naku da aka ƙwamushe.

Ammafa kada kuga an hacking maku facebook kun samu nasarar dawo da shi cikin sauki hakan ya sanya ku riga sakaci da password naku, ko wasu muhimman bayanan da suka danganci account naku,

Dole kuyi kokari ku tsaurara wa facebook account naku tsatstsauran tsaro, ta hanyar yin hakan kuwa kada ku yarda kuyi amfani da password naku na facebook a wata kafar daban, in ba facebook ba ya kasance password din facebook din ku dabanne dana kowanne account naku na kafar sadarwa.

Hakan ba karamin taimakawa zai ba wurin baiwa account naku tsaro, sannan dakwai wani tsarin baiwa account tsaro na facebook mai suna Two step verification 
Wanda babu tayadda wani daban ko kai kanka zaka login a facebook account naka batare daka saka wasu code ba , shi kuwa code din facebook ne zasu turo ma shi ta layinka a sanda ka bukaci kayi login, kuma code din yana expire a minti guda kacal,

Dakwai sauran hanyoyin tsaurara account da dama zamu kawo maku su nan bada dadewa ba 

Mungode

Saturday, February 29, 2020

Hanyoyi goma da zaku Kare katin cirar kudinku (ATM CARD) daga sharrin yan yahoo boys
Assalamu'alaikum jama'a

A rayuwar da muke ciki a yanzu technology ya samu karbuwa sosai a duniya, mutane da dama yanzu zaka samu sun aminta da ajiyan kudi a banki bisa kan su ajje a gida don kuwa suna da tabbacin cewa banki yafi gida tsaro


A cikin kashi dari na mutane zaku samu kashi casa'in da tara na da asusun (account) banki wanda suke ajjiye kudadensu a can,  


Hakanan a cikin kaso dari na  wayanda suka bude asusun banki zaku samu kaso casa'in da tara duk da katin ATM suke amfani wurin cirar kudadensu a banki, duk da cewa a kwai masu amfani da cheque da withdrawal slip, ammana masu amfani da ATM sun fi su yawa, 


Katin ATM yana zamantowa tamkar shine akalar bankinka domin kuwa a kowanne lokaci izan ku ka bushi iska zaku iya tafiya ku ciri kudi, koda kuwa ace sha biyun dare ne, sabanin cheque da shi dole sai lokacin da banki ke aiki sannan zaka ciri kudi da shi, 

nadaga cikin babban dalilin dayasa mutane da dama suka fi amfani da ATM bisa kan cheque


Tofa sai dai dakwai babbar kalubale daya tun karo mu gadan gadan na yaduwar wasu bata garin mutane wai su (yahoo boys) ko (fraudster) duka sunayensu ne, wayannan mutane suna amfani da ATM din mutum su ciri kudaden bankinsa batare da saninsa ba hakanan wani lokacin ba baza ka ga Alert na an debi kudin ka ba sai dai kawai ka farga kaga asusunka babu taro bare sisi.


Yahoo boys na samun daman yin hakanne ta hanyar samun bayanan dake rubuce a jikin katin ATM dinku, wanda da zarar sun ga bayanan shikenan sun samu account naka a hannunsu, sai yadda suka ga dama


Insha Allah zan baku hanyoyi guda goma wayanda na tabbata muddin kuka bi sannan kuka kiyaye da yardan Allah macuta Yahoo boys bazasu samu Nasara akan ku ba

1. Kuyi kokari ku rika sabunta bayanan bankinku akai akai musamman ma Nambar waya,Adireshin Email, Addireshinku da sauransu wanda kuka baiwa bankin yayin register naku, hakan zai taimaka wa bankin matuka wurin sanar daku duk wani shiga da ficen kudi a asusunku

2. Ku kare kanku daga sharrin yan kutse madan datsa, nasu satar bayanan mutane, dakwai darasin mu da mukayi akan hakan yana da kyau ku karanta shi ga darasin nan YADDA ZAKU KARE KANKU DAGA YAN YAHOO BOYS

3. Ku riga taka tsantsan da kasuwancin yanar gizo gizo, sannan izan ma zaku biya kudi ta online to ya kasance kun kulle browser naku, sannan ku kiyaye amfani da hotspot din kyauta wurin biyan kudi a online don ta hakan ma wanda ya bude maku hotspot din zai iya satar bayananku ta na'urarsa batare da sanin ku ba


4. Ku riga duba kudaden dake asusunku akai akai, sannan da transaction history wurinda ake ajjiye bayanan shiga da ficen kudi a susunku,  da zarar kunga abun da baku yarda da shi ba to kuyi maza maza ku yi report a bankinku

5. Yana da kyau ku rubuce nambar Emergency din dake bayan katinku a wani takarda ku ajjiye, koda katin naku ya bace ko an sata sai ku kira nambar kuyi masu bayani

6. In zakuyi tafiya zuwa kasar waje wato in zaku bar Nijeriya kuma ya kasance kana son ka tafi da katinka na cirar kudi, to yana da kyau ka sanar da bankinka ranar da zaka tafi da kuma kasar da zaka tafin


7. A duk lokacin da zakuyi amfani da katin cirar kudinku yana da kyau ku duduuba jikinsa, sannan ku girgizashi ko ma ku shashshare jikinsa da hankicif, sabida yanzu macuta yahoo boys sukan samu kankanin camera su jona a jikin katin cirar kudin mutane, da zarar kun saka katin a cikin ATM machine, katin zai shige ciki Camera din kuma zai fita sabida bazai iya shiga ramin ATM card ba, camera din zai iya faduwa a gefen hannunka ya recording PIN dinka izan zaka saka.


8. Ku riga ankarewa da mutanen dake zagaye daku izan zaku ciri kudi a ATM machine, domin kuwa wasu ba sunzo ciran kudi bane, zuwa sukai su saci bayanan katin duk wanda Yai sakaci da katinsa, shi yasa ake son koda yaushe katinka ya kasance a cikin aljihunka ko wallet naka, ku ki yaye da fitarda katinku a cikin jama'a,  koma zaku fito da katin to ku rufe wurin nambar katinku, da expire date gamida CVV domin wayannan abubuwa uku su kadai macuta ke bukata yayin sankamar kudadenku,  sannan izan zaku sanya PIN a ATM Machine ku kakkare hannunku don kada wani ya ga pin na ku.


9. Kada ku yi gangancin sanar da wani PIN dinku koda kuwa waye shi a wurinku kai koda ma yayankune domin zai iya yiwuwa suyi ganganci macuta su samu daman ganin bayanan ku,  zaifi kyau ku bude masu nasu asusun da su rika amfani da naku

10. Izan katinka yayi expired ka sabunta ka tabbata ka lalata wancan na farkon, a shawarata ma ka samu fetur ka zubawa wancan ka cinna mai wuta shikenan

Daga karshe dai hanya mafi sauki da zaku kare katin cirar kudinku shine ku applying ATM card,  a banki mai tsatsatsauran tsaro.


Thursday, February 27, 2020

Yadda zaku dauko video DAGA YouTube zuwa kan wayarkuAssalamualaikum jama'a
KWANA biyu kun ji mu shiru babu wani tutorial to ai Mana hakuri ayyuka ne suka Dan rincabe Mana Amman yanzu Kam Alhamdulillah

To kamar yadda dai Kukaga title din akan yadda zaku dauko video a YouTube 

YouTube babbar kafar sada zumunta ce ta Duniya wadda ake aika sakonni cikin vidiyo, sanin kankune yanzu idon kowa ya waye da YouTube tsofaffi ma shiga suke su kashe kwarkwatar idanuwansu, sannan a YouTube yanzu zamani yazo da zaka it's koyan abubuwan da dama a YouTube musamman ma ku Mata, DOMIN kuwa a YouTube zaku samu channel suna koyarda yadda ake girke girke,kwalliya da dai sauransu, hakanan ga abubuwan fasahan zamani da ake koya dukka a YouTube, 

Uwa uba ma Comedy wato wasan barkwanci, tunda ga kan Ali artwork,Mazaje Bushkidoo, da sauransu comedians dukka suna da channel a YouTube Wanda akullum zaku samu suna Dora vidiyoyinsu na barkwanci da Shan dariya,  

Sannan yanzu likkafa taci gaba fina finan hausa da sauran shirye shiryen gidajen talabijin duk zaku iya kallonsu a youtube kuma fa kyauta batare da ka biya ko kin biya kosisi ba

Tofa sai de dakwai wani abu dake ciwa mutane tuwo a kwarya gameda youtube shine basa bari mutum yai downloading vidiyo wato ya sauke vidiyo a wayarsa sai dai ya kalla a youtube din ya barshi,  wannan abu kam ba karamin damun mutane yake ba, 

To Alhamdulillah ayau zamu kawo maku sassaukar hanyar da zaku yi downloading vidiyo a youtube duk da basa bari amma zakuyi 

Tom da fari dai ku tabbata kuna da data a wayarku sai kubi wannan link din na kasa zai ku inda zaku downloading application na vidmate, Bayan kun download ku installing sai ku bude bayan kun bude zaku ga vidiyoyin turanci sai kuje wurin searching ku rubuta sunan duk bidiyon da kuke son ku dauko, take zasu baku bidiyoyin sai ku latsa kan wanda kuke son daukowan ku rike hannunku akai na tsawon dakiku zasu nuno maku abubuwa guda biyu try download, da open in new tab sai ku latsa kan try download nan zasu nuno maku wurin download din, inda zakuga format da dama kowanne format na dauke da girman MB nashi sai ku zabi wanda kuke so ku latsa kansa hikenan vidiyon zai fara downloading.