Assalamualaikum fatan Kuna cikin koshin lafiya a yau Kam zamuyi magana nee akan abubuwan Daya kamata mu kiyaye aikatawa izan wayarmu tana chaji

Dakwai wasu abubuwan da mukeyi izan muka sanya wayarmu a caji Wanda wannan Abu ba karamin hatsarine ga wayartamu da Kuma lafiyar mu ba
Wannan Abu kan janyo rashin karfin battery zuwa lalacewar waya da wuri hasalima zai iya janyo wa wayartamu tai bindiga Wanda hakan hatsarine ga lafiyarmu
Ga jerin abubuwan da bayanai akansu

YIN CHARGI DA KOWACCE IRIYAR CHARGER

Yin charging da kowacce iriyar charger hatsarine ga lafiyar wayarmu data batarinta, kusan yawanacinmu bamu damu da charji da kowacce iriyar charger ba mudai kawai muddin waya zatai chargi tofa babu ruwanmu da kalar charger din da muka sakamata Wanda hakan na ragewa batiri karfi, zaifi kyau mu nemi charger din wayar, izan ma zakai da kowacce iriyar charger to kafara duba (currentA) da mafitar Voltage (v) nata don sanin karfin charging charger din

AMFANI DA CHARGER MAI SAURIN CIKA WAYA

Maganar gaskiya anan shine babu Wanda ke chargi ya runga shigar wayarsa ahankali tamkar bazai shiga ba, to Amma inajin yafi kyau muyi hakuri don hausawa sunce Mai hakuri shike dafa dutse har yasha romonsa,

Kowa nason charger Mai CIKA way da wuri, Wanda izan ways tana 6% da kasa zuwa minti biyar zata koma 50% zancen gaskiya shine charger Mai CIKA way da wuri babu abunda take haifarma waya face ta lalata karfin battirin ka sabida ire iren chajar din suna daukene da voltage Mai karfi Wanda daga karshe zai Fara Santa wayarka tana daukar zafi,

So muddin Muna son wayarmu tai karko tofa dolenmu mu guji caji da chaja Mai cika ways cikin mintuna 30 ko 20 

YIN CAJI DA GIDAN WAYA (CONDOM) ko (CASE) a jikinsa

Gidan waya ba karamin kare wayoyinmu yake daga hatsari ba musamman ma faduwar waya a kas,
To Amma izan ya kasance zamu Sanya wayarmu a caji mukan manta da cireshi daga wayar Wanda hakan ba karamin hatsarine bane ga wayar tamu,
Domin kuwa dumin da ke jikin wayarmu bazai samu Daman fita cikin sauki ba sakamakon gidan wayar ya taresa, Wanda hakan zai it's janyo tarwatsewar wayar
Sai mu kiyaye Sanya gidan ways yayin chaji

KWANA ANA CAJI


Kusan dukkanmu Muna da wannan dabi'a ta barin ways ta KWANA tana caji, ba karamin abin Dadi bane ace ka kwanta wayarka na 0% ka farka ka sameta 100% Sai dai Kuma babban hatsarine ga lafiyar wayar don tana daukar zafi sosai inda Nan take karfin battirin ke raguwa 
Yana da kyau mu runga cire wayoyinmu a caji da zarar sun cika

YIN GAME KO FACEBOOK YAYIN CAJI

Wasu abun yabi musu jiki da zarar suna buga game ko Facebook caji ta kare tofa bazasu hakura ba Sai de su Sanya wayar a caji su cigaba da sha'aninsu
Hakan kuwa babbar hatsarine ga lafiyar su data wayar, domin hakan kan iya janyo wayar tayi dumi batiri ya lalace, kana Yana janyo waya taki yin caji da wuri

YIN CAJI DA SAURAN CAJI A WAYA

Wasu sunfi ganewa kowanne lokaci su runga Sanya wayar su a caji Sai kaga waya tana 70% ko 50% Amman sakata a caji, in laifin ma ka bari yakai 25%
Masana kimiyya sun sanar cewa yawan yiwa way caji na rage NAGARTA gamida karkon waya 

ANA CAJI DA POWER BANK KUMA ANA AMFANI DA WAYAR

Kusan abun ya rugaya ya zama ruwan dare a cikin mutane Ana caja waya da power bank kuma Ana amfani da wayar hakan kan janyo wayar ta yi dumi sosai inda inkai wasa ta rage Ma karfin batiri hakanan ya kan Sanya waya Bata karko take lalacewa da wuri
Mungode
Kuyi sharing sannan masu tambaya su ajjiyeta a comment
 

Post a Comment

 
Top