Assalamualaikum fatan Kuna lafiya da yardar Allah yau zanyi maku bayani akan yadda Zaki bibiyi wayarku da aka sace har ku gano  barawon sa'annan ki gano wurinda wayar take,

A zamanin da izan aka sace maka waya tofa saidai Kai hakuri don kuwa inba sa'a kayi ba to har ka mutu bazaka sake ganin wayar taka, to Alhamdulillah yanzu ZAMANI tazo da fasaha ta yadda ake it's bibiyar wayar mutumin da aka sace Kuma a damki barawon

Kusan yanzu zakuga da an satarwa mutum ways Kai tsaye wurin hukuma yake nufa don bibiyi wayartasa inda hukuma zasu cajesa dubu goma Sha biyar, yayin da aka yi nasarar ganin wayar zasu maido masa da dubu goma Sha biyar dinsa da Kuma wayarsa Wanda kuma kudin zasu fito daga hannun Wanda aka Kama da wayarne,

To a irin yanayinnan zaka samu an satarwa mutum ways babba kirar Android Amma Kuma bayada dubu goma Sha biyar din da zaije a bibiyi wayar tasa (tracker), wasu ma izan suka biya kudin wa hukuma da zarar hukuma sun gagara Kama barawon gamida gano yanda wayar take tofa basa dawo masu da kudadensu kudin ya bi ruwa kenan

Izan ya kasance ka samu kanka a cikin Wayanda aka sacewa wa kirar Android ga matakan da zakabi na ganin wayarka ta dawo

Kai tsaye ka samu wata wayar ko ta abokinka koma na waye ka bude chrome ku rubuta www.google.com/android/find ko kuma ku dauko application din FIND MY DEVICE a playstore

Da kun shiga website sin sai ku saka Gmail address da kalmar sirri (password) naku dake jikin waccan wayar da aka sace maku,

Da zarar ya shigar da ku ciki zaku ga sunan waccan Wayartaku da aka sace a gefe guda sai ku latsa kansa sannan Google zai Fara binciken inda mazaunin wayar da aka satar take a wannan lokaci, baya daukan wani lokaci wurin you binciken yake iddarwa
Anan take zakuga wurin da wayarku take wato location, abun babu wahala

Amma kafin ku Fara bibiyar wayarku a yayin da kuja tabbatarda an satar maku waya, Kai tsaye ku Fara tuntubar bankinku day su kulle simcard din daga aiwatar da duk wani transaction, saboda ta hanyar simcard dinku za'a iya gano nambar BVN naku Kuma a ciri muku kudade ta bankinku Amma da zarar kun sanarwa da banking naku zasu dakatar da duk want transaction da nambar sannan su canza maku sabon namba

Fatan darasin namu zai taimaka sosai
Izan da Mai tambaya ya ajjiyeta a comment anan kasa

Next
Newer Post
Previous
This is the last post.

Post a Comment

 
Top