Assalamu'alaikum da yardan Allah yau zamu fara darasi akan yadda zaku gina website naku na kanku a shafin gina website (webbuilder) na wapkiz.

Wapkiz dai webbuilder ne da zai baku daman hada hadadden website a kyauta sannan kuma ku samu kudi da website din, kusan yawancin webmaters da kuke gani yanzu sun fara ne da kananun webbuilder irinsu wapkiz,xtgem da wapka, mywapblog da dai sauransu kafin su koma blogger da WordPress

Ayanzu dai wapkiz shine best free webbuilder in the world duba da yadda yake da sabbabbin features kuma yake baiwa mutum daman saka tallan Adsense sabanin wasu webbulider din da vasa taba yadda a sanya tallan adsense a shafukan da aka kirkira da builder nasu.

Zamu fara darasinne akan yadda zaku hada Download website, wato shafin yanar gizo gizo da ake dora fayil fayil, irinsu wakoki,vidiyoyi,aplications da dai sauransu

Da fari kuje browser naku ku rubuta http://wapkiz.com zai kaiku shafin sai ku taba kan register dake a sama 


Daga nan zai kawoku wurin yin register din zakuga form sai ku cika da bayananku kaman 


Sai ku danna maballin Creat Now
Zai sake kawo ku wani wurin inda za a bukaci ku sanya sunan website din da kuke son budewa da short description nashi da kuma category na shafin, a wurin subdomain ku zabi wapkiz.com tayadda za arunga ziyartar shafinku kamar haka www.shafinku.wapkiz.com .

Kai tsaye bayan kun latsa maballin Creat Now zai kawoku panel na website naku inda a wurinne zaku fara designing website dinku, sai kuyi kasa kuje kan preset (template) 

Zai kawoku wurin template din sai ku zabi Download site tunda dama download site ne muke kokarin hadawa, Ku danna maballin Apply sannan Zai dawo daku shafinnaku inda zakuga shafin a ciki  design mai kyau


Sai ku tsumayemu a kashi na gaba wanda zamuyi bayanin yadda zaku dora wakoki da vidiyoyi da kuma yadda zaku bude category wa kowanne fayil

Post a Comment

 
Top