Wednesday, January 1, 2020

Home Kuna son sanin wake bibiyan (tracking) wayarku

Wayar Android wayace ta zamani data zo da abubuwan karuwa da dama, yawancin dalilan daya sanya mutane suke zaban wayar Android saboda features nata,  a dacan ana amfani da waya don kirane kawai (voice communication) ammafa yanzu an wuce babin don a yanzu wani ma in ka bincikeshi zaka samu badon kira bane ya siya wayarsa

Kusan duk wani abu da ake yi a computer na'ura mai kwakwalwa yanzu ana yinshi da wayar Android, kama daga kan design, editing da sauransu, 

Sai dai kuma da kwai wasu kwayoyin cuta dake bibiyan wayar Android wanda sun hada da malware,keylogers, trojans da sauransu wayanda suke lalata wayoyi, 

A irin wannan yanayi tabbatar da tsaron wayarmu itace abu mai muhimmanci, zamu lissafto wasu CODE wayanda zasu taimaka maku sosai wurin ganin SETTING na wayarku,  da sanar daku in wani na bibiyan kiranku, sako da sauransu

*#21#
Wannan code din zai taimaka maku wurin ganin ko ana bibiyan messages, calls da sauran data din wayarku, zaku iya samun bayanan call forwading naku, zaku iya ganin ko fax,sync,packet acces, sms, async da pad access call fowarding suna kunne ko suna kashe.

*#62#
Izan ana kiran nambarka yana nuna No service ko no Answer to ka dialing code dinnan a wayarka ta Android zai taimaka maka wurin sanin inane kiranka (calls) , messages da sauran abubuwan wayar suke tafiya izan an turo,  don kuwa ana iya hada redirected calls or messages, wato izan an kiraka maimakon kiran yazo layinka sai ya wuce layin wanda ke tracking naka,  ta hanyar amfani da code din can zaku iya gane hakan

*##002#
Wannan code din yana kulle gabadayan call forwading, kuma yana tsaida call or message redirection, izan kana fuskantar matsalar call redirection izan aka kiraka kiran na shiga wayar wani wannan na sauraran dukkan maganganun da kake a waya zaifi kyau kayi amfani da wannan code din kafin kayi roaming.


*#06#
Wannan code din da shine ganin (IMEI) International Mobile Equipment Identifier din waya, code dinnan yana da matukar amfani a babban waya, kasancewar yanzu koda an sata waya ana iya gano barawon wayar da taimakon IMEI

*##4636#*#* ko *#*#197328640#*#*
Wannan code din na musamman ne da taimakonshi wani zai iya bibiyan inda kake, sannan ya gane ko ana bibiyanka, misali izan barayi suka kidnapping wani to da taimakon wannan code din za'a iya gano inda wanda aka satan yake, har takai ga an kama barayin

GA YADDA ZAKU GANO INDA MUTUM YAKE

Ku dialing nambar ku shiga UMTS Cell Environment,  sannan ku shiga UMTS RR info. Daga nan sai ku kwashe nambobin dake karkashin cell ID.

Daga nan ku je MAIN MENU ku danna MM info ku zabi Serving PLMN. Sai ku kwashe nambobin dake karkashin Local Area Code (LAC)

Bayan kun kwafe nambobinnan sai ku je website din http://opencellid.org anan zaku iya binciken taswirar inda wayar keda hadaka da, kuma ku gano inda wannan mai wayar yake
No comments:
Write Comment