Jama'a ku kiyaye kwanan nan 'yan yahoo boys sun fidda wata sabuwar hanyar cuta wadda suke kwasar wa mutum kudaden bankinsa da ita.

Da yawa daga cikinmu mun sani sukan kira mutum a waya su ce masa su ma'aikatan bankinsa ne sukan ce wai account naka ya samu matsala dun haka suna bukatan details din account dun su gyara maka,  waddda da zarar ka basu bayanan account naka tofa kai takare maka dun sun runga dibar kudaden account naka kenan har sai sun kare.

Tom yanzu sunga kusan kowa ya gano wancan hanyar da suke bi don cutan jama'a yanzu sunfiddo da sabuwar hanya wanda in baku kiyaye ba zaku iya ruftawa ciki, 

Sabon hanyar da suka fidda shi shine zakuga an turo maku da sakon EMAIL da sunan bankin da kuke amfani da shi akan an cire #2000 naira a cikin account din wai kudin subscription na bank magazines da ma wani bayanin da baka san da shi ba kuma baka nema ba, zasu cigaba da turo maku sakon email din duk karshen wata, wanda kaikuma ta ganin hakan hankalinka zai tashi ka fara tunanin yaushe kayi subscription na monthly magazine da har suke cire maka 2000 duk wata.

A karshen sakon Email din dakwai link din fita daga tsarin subscription din wanda in ka danna kan link din zai kaika wani shafi da zasu nemi ka saka bayanan bankinka kama daga kan account number, suna, banki, da BVN.

Muddin kuka yi gangancin cike wannan form din tofa naku yaja, dun a take zaku fara jin Alert ana zarar kudadenku babu dalili.

YADDA ZAKU KARE KANKU DAGA FADAWA KOMAR YAN YAHOO BOYS

Da zarar kunga sakon EMAIL makamancin wanda nai muku bayaninsa to ku rabu da email din, ko kuje banki ku duba account balance naku, kuga ko an taba,  inma an taba kuyi complain a cikin bankin.

Kada ku fara gangancin danna UNSUBSCRIBE daga link din sakon email din, ni in za kubi shawarata ma da zarar sun turo maku da irin sakon Email dinnan ku runga deleting nashi kawai, 

SHAWARA TA MUSAMMAN DON GUJEWA FADAWA KOMAR YAHOO BOYS

Zan baku shawara ta musamman wanda muddin kukai aiki da ita bana tunanin zaku fada komar 'yan yahoo boys.

Kufa sani duk yadda kuka kai ga wayo gamida taka tsantsan to mai son abunka yafika dabara, inji hausawa hakanan su yan yahoo boys dinnan wallahi basa da maraba da 'yan fashi.

Shawarar da zan baku shine ko waye kuma ko a ina ne,  kama daga kan Facebook, whatssap, instagram, twitter da sauran kafafen sada zumunta kada ku yadda ku baiwa wani bayanan bankinku,  kai koda ma ace ma'aikatan bankinne suke online kada ku basu,  face kunje branch na bankin, kai ko dama wasu kamfani ne suka bukaci ku basu bayanan bankinku kada ku basu,  domin kuwa Duniya ya lalace, mutumin Nigeria da kuke gani wallahi kuji tsoronsa kamar 💥 bomb,  

Inma account naku ya samu matsala kai tsaye sai ku wuce banki kuyi masu complain, 


WANNAN SANARWA NE DAGA JAMI'AN TSARON NIJERIYAPost a Comment

 
Top