Assalamu'alaikum jama'a

A rayuwar da muke ciki a yanzu technology ya samu karbuwa sosai a duniya, mutane da dama yanzu zaka samu sun aminta da ajiyan kudi a banki bisa kan su ajje a gida don kuwa suna da tabbacin cewa banki yafi gida tsaro


A cikin kashi dari na mutane zaku samu kashi casa'in da tara na da asusun (account) banki wanda suke ajjiye kudadensu a can,  


Hakanan a cikin kaso dari na  wayanda suka bude asusun banki zaku samu kaso casa'in da tara duk da katin ATM suke amfani wurin cirar kudadensu a banki, duk da cewa a kwai masu amfani da cheque da withdrawal slip, ammana masu amfani da ATM sun fi su yawa, 


Katin ATM yana zamantowa tamkar shine akalar bankinka domin kuwa a kowanne lokaci izan ku ka bushi iska zaku iya tafiya ku ciri kudi, koda kuwa ace sha biyun dare ne, sabanin cheque da shi dole sai lokacin da banki ke aiki sannan zaka ciri kudi da shi, 

nadaga cikin babban dalilin dayasa mutane da dama suka fi amfani da ATM bisa kan cheque


Tofa sai dai dakwai babbar kalubale daya tun karo mu gadan gadan na yaduwar wasu bata garin mutane wai su (yahoo boys) ko (fraudster) duka sunayensu ne, wayannan mutane suna amfani da ATM din mutum su ciri kudaden bankinsa batare da saninsa ba hakanan wani lokacin ba baza ka ga Alert na an debi kudin ka ba sai dai kawai ka farga kaga asusunka babu taro bare sisi.


Yahoo boys na samun daman yin hakanne ta hanyar samun bayanan dake rubuce a jikin katin ATM dinku, wanda da zarar sun ga bayanan shikenan sun samu account naka a hannunsu, sai yadda suka ga dama


Insha Allah zan baku hanyoyi guda goma wayanda na tabbata muddin kuka bi sannan kuka kiyaye da yardan Allah macuta Yahoo boys bazasu samu Nasara akan ku ba

1. Kuyi kokari ku rika sabunta bayanan bankinku akai akai musamman ma Nambar waya,Adireshin Email, Addireshinku da sauransu wanda kuka baiwa bankin yayin register naku, hakan zai taimaka wa bankin matuka wurin sanar daku duk wani shiga da ficen kudi a asusunku

2. Ku kare kanku daga sharrin yan kutse madan datsa, nasu satar bayanan mutane, dakwai darasin mu da mukayi akan hakan yana da kyau ku karanta shi ga darasin nan YADDA ZAKU KARE KANKU DAGA YAN YAHOO BOYS

3. Ku riga taka tsantsan da kasuwancin yanar gizo gizo, sannan izan ma zaku biya kudi ta online to ya kasance kun kulle browser naku, sannan ku kiyaye amfani da hotspot din kyauta wurin biyan kudi a online don ta hakan ma wanda ya bude maku hotspot din zai iya satar bayananku ta na'urarsa batare da sanin ku ba


4. Ku riga duba kudaden dake asusunku akai akai, sannan da transaction history wurinda ake ajjiye bayanan shiga da ficen kudi a susunku,  da zarar kunga abun da baku yarda da shi ba to kuyi maza maza ku yi report a bankinku

5. Yana da kyau ku rubuce nambar Emergency din dake bayan katinku a wani takarda ku ajjiye, koda katin naku ya bace ko an sata sai ku kira nambar kuyi masu bayani

6. In zakuyi tafiya zuwa kasar waje wato in zaku bar Nijeriya kuma ya kasance kana son ka tafi da katinka na cirar kudi, to yana da kyau ka sanar da bankinka ranar da zaka tafi da kuma kasar da zaka tafin


7. A duk lokacin da zakuyi amfani da katin cirar kudinku yana da kyau ku duduuba jikinsa, sannan ku girgizashi ko ma ku shashshare jikinsa da hankicif, sabida yanzu macuta yahoo boys sukan samu kankanin camera su jona a jikin katin cirar kudin mutane, da zarar kun saka katin a cikin ATM machine, katin zai shige ciki Camera din kuma zai fita sabida bazai iya shiga ramin ATM card ba, camera din zai iya faduwa a gefen hannunka ya recording PIN dinka izan zaka saka.


8. Ku riga ankarewa da mutanen dake zagaye daku izan zaku ciri kudi a ATM machine, domin kuwa wasu ba sunzo ciran kudi bane, zuwa sukai su saci bayanan katin duk wanda Yai sakaci da katinsa, shi yasa ake son koda yaushe katinka ya kasance a cikin aljihunka ko wallet naka, ku ki yaye da fitarda katinku a cikin jama'a,  koma zaku fito da katin to ku rufe wurin nambar katinku, da expire date gamida CVV domin wayannan abubuwa uku su kadai macuta ke bukata yayin sankamar kudadenku,  sannan izan zaku sanya PIN a ATM Machine ku kakkare hannunku don kada wani ya ga pin na ku.


9. Kada ku yi gangancin sanar da wani PIN dinku koda kuwa waye shi a wurinku kai koda ma yayankune domin zai iya yiwuwa suyi ganganci macuta su samu daman ganin bayanan ku,  zaifi kyau ku bude masu nasu asusun da su rika amfani da naku

10. Izan katinka yayi expired ka sabunta ka tabbata ka lalata wancan na farkon, a shawarata ma ka samu fetur ka zubawa wancan ka cinna mai wuta shikenan

Daga karshe dai hanya mafi sauki da zaku kare katin cirar kudinku shine ku applying ATM card,  a banki mai tsatsatsauran tsaro.


Post a Comment

 
Top