Assalamualaikum jama'a
KWANA biyu kun ji mu shiru babu wani tutorial to ai Mana hakuri ayyuka ne suka Dan rincabe Mana Amman yanzu Kam Alhamdulillah

To kamar yadda dai Kukaga title din akan yadda zaku dauko video a YouTube 

YouTube babbar kafar sada zumunta ce ta Duniya wadda ake aika sakonni cikin vidiyo, sanin kankune yanzu idon kowa ya waye da YouTube tsofaffi ma shiga suke su kashe kwarkwatar idanuwansu, sannan a YouTube yanzu zamani yazo da zaka it's koyan abubuwan da dama a YouTube musamman ma ku Mata, DOMIN kuwa a YouTube zaku samu channel suna koyarda yadda ake girke girke,kwalliya da dai sauransu, hakanan ga abubuwan fasahan zamani da ake koya dukka a YouTube, 

Uwa uba ma Comedy wato wasan barkwanci, tunda ga kan Ali artwork,Mazaje Bushkidoo, da sauransu comedians dukka suna da channel a YouTube Wanda akullum zaku samu suna Dora vidiyoyinsu na barkwanci da Shan dariya,  

Sannan yanzu likkafa taci gaba fina finan hausa da sauran shirye shiryen gidajen talabijin duk zaku iya kallonsu a youtube kuma fa kyauta batare da ka biya ko kin biya kosisi ba

Tofa sai de dakwai wani abu dake ciwa mutane tuwo a kwarya gameda youtube shine basa bari mutum yai downloading vidiyo wato ya sauke vidiyo a wayarsa sai dai ya kalla a youtube din ya barshi,  wannan abu kam ba karamin damun mutane yake ba, 

To Alhamdulillah ayau zamu kawo maku sassaukar hanyar da zaku yi downloading vidiyo a youtube duk da basa bari amma zakuyi 

Tom da fari dai ku tabbata kuna da data a wayarku sai kubi wannan link din na kasa zai ku inda zaku downloading application na vidmate, Bayan kun download ku installing sai ku bude bayan kun bude zaku ga vidiyoyin turanci sai kuje wurin searching ku rubuta sunan duk bidiyon da kuke son ku dauko, take zasu baku bidiyoyin sai ku latsa kan wanda kuke son daukowan ku rike hannunku akai na tsawon dakiku zasu nuno maku abubuwa guda biyu try download, da open in new tab sai ku latsa kan try download nan zasu nuno maku wurin download din, inda zakuga format da dama kowanne format na dauke da girman MB nashi sai ku zabi wanda kuke so ku latsa kansa hikenan vidiyon zai fara downloading.
Post a Comment

 
Top