Dandatse (hacking) wa mutane facebook account ya zama ruwan dare kusan kullum da ko yaushe  sai kun samu an dandatse facebook din wani, 

Wasu Mutane na tunanin ko daga facebook ne suke kulle masu account basusan cewa hackers bane ke hacking don biyan wata bukata ta su, 

Yanzu fa da anga kana da followers da friends 5000 kuma kana da friend request a kasa da suka kai 300 tofa ka shiga uku da hackers don sun rika kau ma account naka wafta kenan har sai sanda sukai nasarar wafce Account din a hannunka sannan zasu sami sukuni, 

Nasan mutane da dama zasuyi tunanin to wai ma su hackers dinnan ko da sun hacking account na mutane me suke da shi ko kuma me zasuyi da shi, wani Abokin a facebook ya taba yi min irin wannan tambaya, murmushi kawai nai masa nace da shi ai yanzu a kaf fadin facebook babu wanj abu mai daraja da ake siyansa da tsada kamar Facebook Account da Facebook page .

Abun dake faruwa shine aduk lokacin da aka kwamushe muku account sai a siyarwa wani ko wata ko shi wanda ya hacking din ya ruga amfani da account din,  dakwai darasi mai zuwa da zanyi maku bayanin Abunda ake da account din izan an siya 

Yanzu kam zamu fada kan darasinmu gadan gadan, 

Izan ya kasance ka samu kan ka daga cikin wayanda aka kwamushe musu Facebook Account,  kada ka dami kasha kuruminka kawai ka kwantar da hankalinka ka karanta wannan darasi namu a nutse

Dakwai hanyoyi da dama da ake kwamushe wa mutane Account sannan izan aka kwamushe maka account za a iya canja password din account din

IZAN AKA KWAMUSHE MUKU ACCOUNT KUMA AKA CANZA PASSWORD.

Yawancin hacking facebook account da hackers keyi suna yinsa ne ta hanyar canza password sabida kada mamallakin Account din ya samu damar shiga, balle ma har yayi da shi

Kwato irin wannan Account din daga hannun makwamusa wato hackers abune mai sauki,  wanda Alal hakika yafi komai sauki, kawai kubi wayannan matakai na kasa don dawo da account naku 

MATAKI NA FARKO
EMAIL & PHONE NUMBER

Izan ya kasance password ne kawai aka canza a account din kuma kun connecting Account din da Gmail Adress naku, sannan kuna da daman shiga Gmail din ko kuma Nambar da kuka bude account din yana wayarku 

Sai ku shiga facebook din kuje kan Forgot password , dake kasan facebook login page, 
zai kaiku wani shafin na daban inda zasu bukaci da ku sanya Username, ko Email Adress ,  ko Phone number, naku wanda kuka bude facebook din da shi, 

Bayan kun saka daya daga cikin ukunnan sai ku taba kan maballin continue 

Izan nambar waya kuka sanya zasu turomaku da recovery code ta layinku a SMS sai ku kwafo Recovery Code din ku dawo shafin ku zuba shi, 

Izan kuma Email adress kuka sanya shima zasu tura maku recovery code ta Email naku sai ku minimize kuje inbox na Email naku ku kwafo code din ku dawo facebook ku zuba shi

Bayan kun zuba sai ku taba maballin continue, anan ma zai sake kawoku izuwa wani shafin na daban wanda shi kuma zasu nuna maku inda zaku sanya sabon password,  izan kuka saka sai ku sake sanyawa a akwatin kasa wanda shine na confirm, 

Abun lura,  Yana da kyau yayin saka password ku saka password mai matukar wahala wanda ya hada da manyan Haruffa,ƙananan haruffa, symbol, nambobi, MISALI: E23e45&#s86@)ytech990@$_-;:
Daga nan Kai tsaye zai kai ku want shafi inda zasu nemi kuyi LOGOUT OF ALL SESSION, Ma'anan hakan kuwa shine zakuyi LOG OUT aduk wata waya ko kwamfutar da aka taba login Facebook account naku, na wayan da kake amfani da itace kawai bazatayi logout ba, bayan kunyi hakan zasu nuna maku Activities na account naku, Sai ku duba dakyau duk activities da kukasan baku yi ba Sai ku deleting na shi,

MATAKI NA BIYU

Idan kuma ya kasance bayan maƙwamushin ya ƙwamushe account din ya canza password, naka Sannan ya canza phone number naka, 
Kaga baka da daman yin aiki da matakin farko kenan sai de ka jarabawar mataki na biyu wanda yanzu sanyi bayani akansa,

Manyan maƙwamusa da suka ka san harkar sosai basa ƙwamushe Facebook account batare da sun canja Email,phone number da ma wasu abubuwan ba,

Idan ya kasance ka samu kanka cikin waƴanda aka ƙwamushe musu account kuma aka canja email da phone number to kasha kuruminka 

Kawai ku shiga facebook kuje login page wato shafin shiga, a kasan shafin zakuga forgot password, sai ku taba kansa zasu nuni maku wani Form sai ku saka sunan da kuke anfani da shi a facebook, zai danyi searching kafin ya nuni maku jerin mutane masu amfani da irin sunan da kuka saka sai ku duba hotonunansu zaku ga naku sai ku taba kan hotonku, 

Zasu kai ku wani shafi inda zasu bukaci su resetting password naku, sai ku taba kan “no longer have access to these” , 
Daga nan zasu baku Recovery Option wato sabon hanyar da zasu dawo maku da account, sai de tsarin ya dangata ne da adadin shekarun da ka diba kana facebook, idan account naka yakai akalla shekaru biyar zuwa sama a facebook to zasu baka security questions ne kawai wanda kana amsashi shikenan zasu bude maku account ku canja password

Idan kuma account naka sabone haifi shekara guda ba ko bai watanni uku zuwa hudu zasu baku tsarin "trusted contacts”
Sai ku zuba nambar email address naku da kuke amfani da shi sannan ku danna kan reveal my Trusted contacts,  sai ku sanya sunan daya daga cikin su,
Shin su waye Trusted contacts: trusted contact wasu daddaikun mutane ne da ake zabansu a matsayin Amintattun Mutane, wanda amfaninsu shine izan facebook account naka ya samu matsala ko aka hacking zasu taimake ka wurin dawo da account din , kuma dai kaine zaka zabi waƴannan mutane daga cikin Abokanka, wasu daga cikinku sun san yadda ake zaban mutum a matsayin Trusted contacts wasu kuwa basu sani ba to kada mu damu nan gaba kadan zanyi bayanin yadda zaka zabi wani a matsayin Trusted contacts dinka
Bayan kun saka sunan daya daga cikin Trusted contact naku facebook zasu tura masu da link sai ku bukaci su bude link din su dauko maku code din security code da suke nema, bayan sun fada maku sai ku saka code din a muhallin da shi kenan

MATAKI NA UKU 
Idan ya kasance maƙwamushin daya ƙwamushe maku account ya canza Email facebook zasu aiko maku da sako a tsohon email naku zasu sanar daku kokarin canza email din da ake yi a kasan sakon zakuga sun rubuta "if you did not do this, please secure your account" sai ku taba kan rubutun zasu kawo ku inda zaku tsaurara tsaron Account naku, 
Sannan zasu baku hanyoyin dawo da account nakun,

 HANYAR FARKO

Hanyar farko shine ku dora Katin shaidar gwamnati, wanda zai iya zama , katin zabe, voters card, national Id card Katin ɗan kasa, da dai sauransu duk dai ID card din Daya shafi gwamnati zaku iya dorawa
Bayan hakan facebook zasu bude maku account naku kana su baku daman canza password

HANYA TA BIYU

Hanya ta biyu itace facebook zasu bukaci ku sanya shekarun haihuwar ku, wata, da kuma rana, kamar dai yadda kuka sanya a profile naku izan dai wanda kuka saka yayi daidai Dana profile naku zasu bude maku account din kana su baku daman canza password

HANYA TA UKU

Hanya ta uku kuwa facebook zasu shiga profile naku su dauko hotunan Abokanka su rika nuna maku ɗaya bayan ɗaya, abinda suke bukata shine duk hoton da suka nuna maku to aka san hoton akwai Option Mai dauke da sunaye biyar zuwa shida, sai ku zabi sunan Aboki ko ƙawarku dake jikin hoton a cikin Option dinnan Wanda Kuma sunan yazo daidai dana hoton, izan kuka zabi sunayen Mutane biyar daidai shi kenan zasu bude maku account su nemi ku canja password.


Idan ya kasance kun gwada duk wa'yannan matakai da hanyoyin dana lissafo amma baku samu nasarar dawo da account naku ba tom akwai wasu sabbin hanyoyi da facebook suka fitar da su kwanan nan akan matsalar hacking wa mutane facebook account, ga sabbin hanyoyin a nan kasa.

SABUWAR HANYA TA ƊAYA

facebook sun fitar da sabuwar hanyar dawo da account din da maƙwamusa suka ƙwamushe ta hanya mai sauki wanda a wani lokacin ma ba sai kayi verification ba kawai abinda ake bukata shine kayi resetting password naka a cikin wayar da mafi shigar facebook da ita, wato wayar da akullum da ko yaushe kake shiga da ficen facebook da shi, misali;
Ka kai tashin shekara guda ko wata uku kana amfani da infinix smart 2, to Kuma rana tsaka sai aka ƙwamushe maka account, to muddin kana bukatar ka dawo da account naka cikin sauki sai ka shiga facebook ta infinix naka nan facebook zasu recognizing wayar taka, wato zasu gane ta tunda dama can da itace ka saba shiga, zasu tabbatar da kaine ba wani ba

Hakanan ma izan ya kasance mafi shiga facebook da wifi to sai kayi amfani da wannan wuri din da ka saba shiga da shi wurin resetting password din

SABUWAR HANYA TA  BIYU

kwanan nan facebook suka samar da wani tsari wai shi identity verification 
Da wannan tsarin zaku iya dawo da ƙwamusashshen account naku ta hanyar turawa facebook (government ID) wato shaidar tabbatarwa ta gwamnati kamar voters card, national ID card ,driven license da dai sauransu bayan kun tura facebook zasu duba bukatar ku na tsawon kwana ɗaya zuwa kwana uku sannan su taimakeku wurin dawo da account naku daka ƙwamushen cikin sauki, muddin kuka bi wa'yannan matakai na kasa

Ga matakan da zalunci wurin tura masu da Government ID naku:
Zai kaiku wani shafi sai ku cike dukkan Form din da suka bukata sannan ku dora government ID naku, 
Bayan kun cike sai ku tura Form din zuwa facebook ku tsumayesu na ɗan kwanaki
Daga nan facebook zasu turo maku da sakon Email mai dauke da likau (link) din da zaku bi ku dawo da account na ku sannan ku canza password

Waƴannan hanyoyi da matakan da mukai bayani akan su sune hanyoyin da zaku bi wurin dawo da facebook account naku da aka ƙwamushe.

Ammafa kada kuga an hacking maku facebook kun samu nasarar dawo da shi cikin sauki hakan ya sanya ku riga sakaci da password naku, ko wasu muhimman bayanan da suka danganci account naku,

Dole kuyi kokari ku tsaurara wa facebook account naku tsatstsauran tsaro, ta hanyar yin hakan kuwa kada ku yarda kuyi amfani da password naku na facebook a wata kafar daban, in ba facebook ba ya kasance password din facebook din ku dabanne dana kowanne account naku na kafar sadarwa.

Hakan ba karamin taimakawa zai ba wurin baiwa account naku tsaro, sannan dakwai wani tsarin baiwa account tsaro na facebook mai suna Two step verification 
Wanda babu tayadda wani daban ko kai kanka zaka login a facebook account naka batare daka saka wasu code ba , shi kuwa code din facebook ne zasu turo ma shi ta layinka a sanda ka bukaci kayi login, kuma code din yana expire a minti guda kacal,

Dakwai sauran hanyoyin tsaurara account da dama zamu kawo maku su nan bada dadewa ba 

Mungode

Post a Comment

 
Top