Gmail account abune mai matukar amfani a rayuwar wannan zamani domin kuwa kusan duk wani abu da zaka ga anayi zaka samu ana bukatan email address,

Kamar jamb,bude account na banki da dai sauransu, kafin mu tafi ga darasinmu gadan gadan zamu ɗan yi gajeran bayani akan muhimmancin Gmail dama amfaninsa

Da farko menene EMAIL

 A turance izan aka ce EMAIL a na nufin Hanyar aika sakonni daga wani wuri zuwa wani wuri ta hanyar amfani da na'ura ko ince lantarki

Dakwai kamfanoni da dama dake bada daman mallakar Email cikinsu kuwa akwai gmail,yahoomail,hotmail e.t.c 

In Allah ya yarda muddin kuna tare da mu duk zamu yi maku bayani dalla dalla akan yadda zaku bude Email da kamfanoni da muka lissafo a nan sama, amman bari mu fara da Gmail

Muhimmancin Email 

Kamar yadda na fada maku ne a sama cewa Email yana da matukar muhimmanci domin kuwa yanzu babu shafin da zakaje kayi register ko joining nasu batare da ka sanya email naka ba don su rika aiko maka da sakonni, 

Ku dau misali da JAMB, sanin kanku ne dole sai mutum yana da Email address sannan ake bude masa jamb, to amman kun taba yin tunanin dalilin ya sanya ake bukatar Email a Jamb, 

Babban dalilin daya sanya jamb ke bukatar Email naku shine don turo maku da sakonni, in baku manta ba na sanar daku Amfanin email dama kenan turo da aika sakonni ta internet, ta email naku jamb zasu na tura maku duk wasu informations daya danganci jamb account naku bama tare da kunje portal nasu ba

Kuna da sanin da cewa a facebook izan kuka sanya Email naku zasu rika turo maku da duk wani activities da kukayi a facebook ta Email inbox naku, a takaice dai Email kamar SMS yake ta wani fannin ma yafi SMS amfani dun shi international ne a kowacce kasa zaka iya amfani da ita sannan daga kowacce kasa za'a iya turo maki da sako ta cikinta kuma zaku iya turawa

Menene GMAIL

Gmail na nufin GOOGLE MAIL wato kamfanin aika sakonnin EMAIL na Google kusan a duk gabadayan kamfanonin Email na duniya mutane sunfi amfani da gmail, sannan koda ma ace mutum yana amfani da yahoomail ko hotmail kai kuma kana amfaninda gmail zaka iya tura masa sako babu damuwa

Yadda zaku bude account da gmail

Da fark kubi link dinnan 
https://accounts.google.com/signup/v2/webcreateaccount?flowName=GlifWebSignIn&flowEntry=SignUp
Zai kaiku wani wuri kamar haka

Sai ku cika form din 
A akwatin farko zaku sanya sunanku kamar yadda kukaga na saka

Akwati na biyu kuma sai ku sanya sunan babanku 

Akwati na uku kuma sai ku rubuta yanda kuke da bukatan adireshin gmail din ya kasance misali kamar shuraihu009@gmail.com

Akwati na hudu kuma wurin saka password ne (kalmar sirri)

Akwati na biyar zaku maimaita kalmar sirrin da kuka sanya a akwati na hudu don tabbatar da kun saka daidai

Daga nan sai ku danna maballin next zai kawoku wanni shafi makamancin hoton kasannan


Akwatin farko zaku sanya nambar wayarku

Akwati na biyu kuma zaku sanya Recovery Email Naku
Recovery Email: na nufin wani Email wanda yake naka ko na Abokinka, koda an samu akasi ka manta password din wannan email din naka zasu bukaci ka sanya Recovery Email din daka saka a anan  ko kuma izan ana kokarin ai maka hacking Gmail in mutum baisan Recovery Email naka ba dole yayi hakuri, 
Izan bakwada da wani Email din sai kubar wurin empty batare da kun saka komai ba

Abu nagaba shine Shekarun haihuwarku,
Da farko zaku saka watanni a karkashin akwatin month, sai ranan da aka haifekun a karkashin akwatin days shekarun kuma akarkashin years
Misali: 11 - 04 - 2000

Abu nagaba shine ku zabi jinsinku, 

Abun lura: kada kuyi gangancin saka shekarun karya wanda bana haihurwarku ba, domin kuwa a nan gaba zasu iya bukatar da ku dora government ID naku 

Bayan kun gama saita duk wannan sai ku danna nextA wannan shafin zasu bukaci ku sanya nambar wayarku izan kuka saka zasu turo muku da verification code ta SMS 
Sai kuyi minimize kuje inbox naku ku kwafe code din sa'annan ku dawo ku zuba shi a wurinda suka bukata


Daga nan zasu kawoku shafin samannan sai ku danna kan Yes I'm in

Zasu kawoku wurin dokokinsu kuyi kasa ku danna Agree Kai tsaye zasu kawo ku profile naku kaman haka


A nan zaku iya canza duk  wasu bayanan account din kama daga kan hoto,suna,ranar haihuwa da dai sauransu

Anan muka kawo karshen wannan darasi mun barku lafiya

Duk mai tambaya sai ya ajjiyeta a commentPost a Comment

 
Top