Nasan zaku kasance cikin mamaki da al'ajabin yadda nace zakuyiwa simcard naku na Airtel wellcomed back cikin abunda bai wuci mintuna biyar ba

Bayanai ne daki daki zanyi wanda muddin kuka bi bayanan nawa zaku kai ga ci,
Shin Airtel sim naka ko naki ya bace ko ya lalace kuma kuna da bukatar dawowa da shi don cigaba da amfani da layin tom sai ku girgije idanuwanku ku karance wannan darasi tsaf tun daga farko harya zuwa karshe, don sanin yadda zakuyi wellcomed back da kanku cikin mintuna biyar batate da kunje branch na Airtel ba kuma batare da kun kira customer care ba

Abun da kawai kuke da bukatar aikatawa shine tura sakon SMS ta hanyar bin bayanan da zanyi a nan kasa shi kenan bukatarku zata biya

ABUBUWAN DA AKE DA BUKATA

  1. wayar da zata iya tura sako SMS
  2. Sim pack din Sabon layin Airtel
  3. Sim pack din tsohon layin Airtel wanda zakaiwa welcome back

Bayan kun tabbata kuna da abubuwan dana lissafo a anan sama sai kuje wurin tura sakon SMS a wayarku ku rubuta:

SUNANKU (sai ku bada gab) NAMBAR WAYAR DA ZA'A SANAR DAKU IZAN YAYI (sai ku bada gab) NAMBAR WAYAR DA KUKE SON KUYIWA WELCOME BACK DIN (ku sake bada gab) SERIAL NUMBER NA TSOHON LAYIN (ku bada gab) SERIAL NUMBER NA SABON LAYINKU (ku sake bada gab) PUK NUMBER NA TSOHON LAYIN (ku bada gab) PUK NUMBER NA SABON LAYIN (ku bada gab) NAMBAR WAYAR SABON LAYIN DA KUKA SIYO
bayan kun gama rubutawa Alura da kyau wurinda kukaga na saka (ku bada gab) ina nufin ku bada space kada ku harhada rubutun sannan kada ku saki layi
PUK NUMBER da SERIAL NUMBER zaku samesu a jikin Sim pack na layinku.

 Bayan kun gama sai ku tura rubutun zuwa 190 , ku tabbatar da bakuyi kuskure ba, service din kyautane bazasu cajeku sisi ba, bayan kun tura Airtel zasu yi maku sauran aikin
Ga wayanda haryanzu basu gama fahimta ba to ga misali a nan kasa na yadda zasu rubuta sakon.

Shuraihu Usman 08022220000 07020000022 87390123400010003232 89235678900100400012 78765699 685455555 08021111122

Bayan kun tura zai dau sa'o'i 24 zuwa 48 kafin su bude maku layin 
Kutabbata da kun saka nambar da zasu tuntubeku izan suka kammala,
Ku more sassaukar welcomed back naku

Post a Comment

 
Top