Showing posts with label online business. Show all posts
Showing posts with label online business. Show all posts

Sunday, January 5, 2020

Alamomin da zaku gane kasuwancin Bogi scam a internet
Kamar yadda na sha nanatawa, a intanet ana samun kudi sosai idan an yi da gaske. Wasu kuma suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna da wayon da suke yi su raba jama'a da abin hannunsu da sunan kasuwancin intanet. Masu irin wannan dabara suna da hanyoyi da yawa barkatai, har ma wani lokaci su ci da buguzum a dauka na gaskiya ne.

A yau na zakulo wasu daga hanyoyin da mutum zai yi wa kansa hukunci ya gane ko nau'in kasuwancin da aka bijiro masa na yi ne ko na bari. 
Ga su kamar haka:


1. Abubuwan da ake sayarwa: Idan ka ga yawancin kayan da ake sayarwa ba wasu fitattu ba ne, watakila ma ba wadanda ake iya gani ba ne. Wasu na kiransu 'Packages' ko 'Bundles' ko 'Subscription'. Yawanci babu wani abu a ciki sai zunzurutun shiririta. Da za a ce ka nuna abin da aka sayar maka ko irin aikinsa ba za ka iya ba.


2. Kankanin Kudi Babbar Riba: Daga yanayin ribar da aka yi alkawarin samu za ka fahimci akwai lauje cikin nadi. Duk wani kasuwancin intanet da yayi alƙawarin samun ninki biyu ko fiye na abin da ka zuba cikin wata daya, ka yi nesa - nesa da shi.


3. Shigo da wasu: Shi ne tsarin da ake kira 'Referral'. Watau za a ce idan ka kawo wani yayi rijista ta karkashinka za a baka wani abu na awalaja. Manyan kamfanoni fitattu kamar paypal da ebay da AliBaba da su Quickteller na nan Nijeriya duk suna yin haka, amma ba haka ta ci barkatai ba. Idan ka ga website na yin kasafin adadin kudin da za ka samu idan ka kawo mutane kaza zuwa kaza, lallai abin gudu ne.


4. Rijistar Kamfani: Kamar yadda muka san kamfanonin zahiri suna bukatar a yi musu rijista da hukuma, haka ma kamfanonin intanet. Kowanne kamfani akwai irin rijistar da ta kamace shi. A Nijeriya dai, bayan rijista da CAC, wajibi ne kamfani mai hada hadar kudi ya yi rijista da SEC matukar yana da mutane 50 ko fiye da suka zuba kudinsu a cikinsa komai kankantar kudin.


5. Shugabanni da Jagororin kamfani: Idan ka ga kamfani ya boye sunayen shugabanninsa an rumbun bayanai na Whois, to ka guje shi. Daga nan ne ake gane inda aka dosa har a iya tofa albarkacin baki. Kodayake, wasu na yin dabara su rubuta bayanan bogi a cikin rumbun. Don haka sai an kula kafin a saki jiki da su.


6. Takardun Shaida: A Nijeriya, wajibi ne ga kamfani ya karbi wasu takardun bayanai daga masu son zuba hannun jari a cikinsa. Takardun shaidar sun hada da katin shaida, hoton mutum da BVN da katin dan kasa da kuma takardar biyan kudin ruwa ko wuta ko wata takardar shaida da ke nuna adireshin mutum. Watau irin takardun da ake bude asusun banki da su. Duk kamfanin da ka ga ya kasance daga buhu sai tukunya, watau daga ka yi rijista da su ka zuba kudi sai kurum ka saurari 'alert', to abin gudu ne.


7. Ka'idojin Rubutu: Yawancin kamfanonin kasuwancin bogi ba su damu da rubutu cikin ingantattun hanyoyin ka'idojin rubutu ba. A kowane yare suke rubutun za ka ga kura-kurai barkatai tare da saka kalmomin da basu dace ba. Illar haka shi ne rasa martaba a farfajiyar duniyar google ta fuskar SEO. Wannan su ba damuwar su ba ne, saboda masu taya su tallan kamfanin suna iya isar da sakon da ake bukata ta kafafen soshiyal midiya.


Ba duka aka taru aka zama daya ba, ko anan Nijeriya akwai kasuwancin intanet mai riba sosai wanda ba gara ba zago. Ni ma na zuba a wasu daga cikinsu. Wadannan kamfanoni sun hada da I-Invest, Payday, Elixir, AlatNg da sauransu. Kowacce rana hukumar SEC tana bibiyar ayyukan wadannan kamfanonin, ta yadda koda sun durkushe mutum zai iya maida asarar da ya yi.

Daga Danladi Z Haruna