Showing posts sorted by relevance for query free. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query free. Sort by date Show all posts

Sunday, December 29, 2019

Free browsing, kyautar data ga duk mai amfani da MTN da AIRTEL

Assalamu'alaikum

A yaune kamfanin opera suka sanar da zasu na bada kyautar data ga duk wani mai amfani da layin MTN ko AIRTEL, dun nuna farin cikinsu na shigar SABUWAR SHEKARAR 2020 NEW YEAR

Garabasar datan zai gudana ta cikin application nasu ne mai suna opera with free vpn.

Zaku iya shiga ko ina da datan sannan zaku iya dauko dukkan abunda kuke sa muradin daukowa amman ta cikin opera with free vpn.

Haryanzu dai basu sanar da ranar da zasu kulle garabasar ba

YADDA ZA'AI KU SAMU DATAN

Da farko ku dauko application din opera with free vpn Anan

DOWNLOAD OPERA WITH FREE VPN

Sannan ku tabbata simcard dinku MTN ne ko AIRTEL dun sune kawai suke da access da Opera

Bayan kun download sai ku bude ku cigaba da browsing kyauta, 
Sannan zaku iya bude application opera News  duka a kyauta, 

Wannan kyautar datan na opera sun kayyade shi izuwa 50 MB daily wato kullum kuna da daman ku sankami data 50 a kyauta, 

Kada kuyi wata wata abokai a kafta

Daga Shuraihu Usman
Inkiya 99%

Friday, December 27, 2019

Yadda zaku samu MB 600 a layin MTN kyauta
Assalamu'alaikum fatan kuna lafiya

Insha Allah yau darasinmu zai tattauna ne akan yadda zaku samu MB 500 ko 100 wasu ma zasu iya samun 600 a layin MTN ta hanyar amfani da MY MTN APP

Kusan kowa yasan manhajar (application) din MY MTN APP,  manhajar mymtnapp dai zai baka daman sayen data, sayen katin waya ta banki da sauransu,  sannan izan ya kasance baka taba amfani da manhajar ba da zarar ka bude zasu baka kyautar MB 500 

Yanzu kuma da kwai wata kyautar MB 100 da suke bayarwa a wannan watan,  wanda koda ace ka taba amfani da application din ko baka taba ba da zarar ka bude zasu baka zunzurutun MB har guda 100 

Izan kuwa baka taba budewa ba  yakasance wannan ne karon farkonka da budewa toh zasu baka MB 500 na budewar da kai sannan da MB 100 kyautar da suke bayarwa na wannan wata kaga izan ka hada ka samu MB 600 kenan 

YADDA ZAKA SAMU DATAN

 Da fari ka tabbata wayarka Android ce 
 Sannan sai ku downloading mymtnapp anan kasa

Bayan kun download na app din sai ku install sannan ku bude, zasu nemi ku sanya nambar wayarku bayan kun saka zasu turo da message mai dauke da  kalmar sirri na lokaci guda  (one time password) ta simcard din sai ku kwafe nambobin guda shida 6 ku dawo application din ku zuba take zasu bude application din.

In baku taba budewa ba a saman app din zaku ga ansaka 

YELLO! YOU HAVE BEEN REWARDED WITH 500 MB FREE DATA
Sai ku danna kan CLICK HERE TO ACTIVATE IT

Daga nan zasuyi maku message akan sun baku data 500mB kyauta sai ku danna *559*4# don duba data din izan kuka duba zakuga 600MB  harda kyautan da sukeyi

Izan kuwa ka taba budewa a saman zakaga an rubuta 

YOU HAVE BEEN REWARDED WITH 100 MB FREE DATA

sai ku danna kan CLICK HERE TO ACTIVATE IT atake zasu baku mb 100 sai ku danna *559*4# don duba MB din 

Duk Abunda baku gane ba ku yi tambaya a comment 

Dakwai wani darasinma na samun data 2GB a mtn kyauta kuma kullum

Thursday, March 5, 2020

[free browsing trick] Sayi data 1.5GB akan 300 Naira da 75MB akan 20 NairaKwana biyunnan fa Kamfanin MTN faso gari da tsarukan sayen data masu rahusa wanda da yawan mutane basu san da su ba

Wannan tsari dai ana kiransa data offers 4ME 
Tsarin Data offers 4ME zai baku daman siyan data din da zamu lissafo a nan kasa


 1. 75MB akan 20 Naira

 2. yadda zaku siya


  kuje dialing pad na wayarku ku dialing *121# sai ku zabi data offers for me zai kawoku wurinda zaku ga jerin data din da zaku iya siya sai ku zabi na daya 1 daga nan zasu ciri 20 naira a balance naku su baku 75 MB tsarin nayi a kowanne layin MTN

 3. sayi 1.5GB akan 300

 4. Yadda zaku siya


  Shima wannan din dai zaku dialing*121# daga nan ku zabi Data Offers 4ME sai ku zabi namban 1.5 GB akan 300 anan take zasu baku 1.5GB sa'annan su zari 300 Naira a kudin lalilatarku (balance)

 5. sayi 4GB akan 1000

 6. Yadda zaku siya


  Kuje dialing din wayarku ku dialing *121# daga nan ku zabi Data Offers 4ME sai ku zabi namban 4GB akan 1000 anan take zasu baku 4GB sa'annan su zari 1000 Naira a kudin lalilatarku (balance)

 7. sayi 700MB akan 500

 8. Yadda zaku siya


  Shima wannan din dai zaku dialing*121# daga nan ku zabi Data Offers 4ME sai ku zabi namban 700MB akan 500 anan take zasu baku 700MB sa'annan su zari 500 Naira a balance naku

 9. sayi 1.5GB akan 500

 10. Yadda zaku siya


  Kuje dialing pad ku rubuta *121# daga nan ku zabi Data Offers 4ME sai ku zabi 1.5GB akan 500 anan take zasu baku 1.5GB sa'annan su zari 500 Naira a kudin lalilatarku (balance)

Sai dai fa ku sani data din nayin tsawon kwanaki 7 ne kacal sa'annan suyi expire

Monday, January 13, 2020

Garabasa daga kamfanin MTN, ku sayi 200MB da 50 naira
Assalamualaikum mabiya wannan shafi.
Kwanan Nan fa MTN Sai sakin Bonanza suke Yi ba kakkautawa, in Baku manta ba dakwai free browsing da akeyi kyauta da layin MTN, mun kawo maku darasin rannanYauwa Kuma bayan wayannan garabasa na data dakwai wasu na dabam wayanda muka kawosu sannan mukai bayaninsu anan haryanzu kuma suna amfani basuyi expire ba, 

To duk da haka mun cewa kwanakin baya mtn sun fidda wani tsarin sayen data mai suna INSTABINGE, wanda ake iya siyan datan 1GB akan 200, 250MB akan 100,  4GB akan 1000,  ga code din siyen datan *131*65# sai shi wannan tsarin na instabinge ba akowanne layi bane yakeyi

Kwatsam sai gashi mun discovering wata sabuwar hanya ta siyan 200MB akan 50 

Da fari ku danna *131*25* sai ku zabi 2, shikenan kun siya 200MB da 50 naira, 

Ammafa ku sani shima dai wannan tsarin kamar instabinge yake bakowanne layi bane keyi.

Tuesday, January 7, 2020

Yadda zaku samu data 150MB a layin MTN ta hanyar Gidimo apk

Kwanakin baya wannan manhaja mai suna Gidimo suka fito inda suke baiwa duk wanda yai register da su data 150MB na MTN kuma ma register dasu kyauta ne in kuna da email an wuce wurin


ABUBUWAN DA AKE DA BUKATA

1. Email
2. Gidimo apk
3. MTN sim
4. Kankanin ilmi


Da fari ku fara dauko wannan manhajar ra gidimo a playstore 

Bayan kun dauko sai ku shiga ku danna SIGN UP zai kawoku wurin register, ku saka

Sunanku
Email dinku
Kalmar sirrinku (password)


Daga nan ku sai ku amince da dokokinsh ta hanyar ticking karamin akwatin kasannan sai ku danna kan SIGN UP shi kenan kunyi register sauran tabbatar da nanbar wayarku 

Kai tsaye nan zai kawoku sai ku taba kan Verify your phone number and get free 150MB 

Zasu kawoku wurinda zaku saka nambar wayar zasu turo verification code ta SMS sai minimixe ku duba inbox na messages naku zakuga sakon verification code din daga facebook sai ku kwashe code din ku dawo apk din ku zuba sannan ku danna verify a nan zasu verifying nambar sai kuyi back ku refreshing page din zasu nuna maku kun yi nasarar verifying nambarku don haka ku ajjiye nambarku su turo maku da 150MB Sai ku saka nambarku na MTN a wurin da suka bukaci ku saka nambar, sannan ku danna ok a take zasu turo maku da mb dari da hamsin kyauta, 

Aha duk wanda ke da tambaya ya yita a comnent

Friday, January 3, 2020

Yadda zaku hada (simple download website) a wapkiz kashi na daya 1
Assalamu'alaikum da yardan Allah yau zamu fara darasi akan yadda zaku gina website naku na kanku a shafin gina website (webbuilder) na wapkiz.

Wapkiz dai webbuilder ne da zai baku daman hada hadadden website a kyauta sannan kuma ku samu kudi da website din, kusan yawancin webmaters da kuke gani yanzu sun fara ne da kananun webbuilder irinsu wapkiz,xtgem da wapka, mywapblog da dai sauransu kafin su koma blogger da WordPress

Ayanzu dai wapkiz shine best free webbuilder in the world duba da yadda yake da sabbabbin features kuma yake baiwa mutum daman saka tallan Adsense sabanin wasu webbulider din da vasa taba yadda a sanya tallan adsense a shafukan da aka kirkira da builder nasu.

Zamu fara darasinne akan yadda zaku hada Download website, wato shafin yanar gizo gizo da ake dora fayil fayil, irinsu wakoki,vidiyoyi,aplications da dai sauransu

Da fari kuje browser naku ku rubuta http://wapkiz.com zai kaiku shafin sai ku taba kan register dake a sama 


Daga nan zai kawoku wurin yin register din zakuga form sai ku cika da bayananku kaman 


Sai ku danna maballin Creat Now
Zai sake kawo ku wani wurin inda za a bukaci ku sanya sunan website din da kuke son budewa da short description nashi da kuma category na shafin, a wurin subdomain ku zabi wapkiz.com tayadda za arunga ziyartar shafinku kamar haka www.shafinku.wapkiz.com .

Kai tsaye bayan kun latsa maballin Creat Now zai kawoku panel na website naku inda a wurinne zaku fara designing website dinku, sai kuyi kasa kuje kan preset (template) 

Zai kawoku wurin template din sai ku zabi Download site tunda dama download site ne muke kokarin hadawa, Ku danna maballin Apply sannan Zai dawo daku shafinnaku inda zakuga shafin a ciki  design mai kyau


Sai ku tsumayemu a kashi na gaba wanda zamuyi bayanin yadda zaku dora wakoki da vidiyoyi da kuma yadda zaku bude category wa kowanne fayil