Friday, January 3, 2020

Yadda zaku hada (simple download website) a wapkiz kashi na daya 1
Assalamu'alaikum da yardan Allah yau zamu fara darasi akan yadda zaku gina website naku na kanku a shafin gina website (webbuilder) na wapkiz.

Wapkiz dai webbuilder ne da zai baku daman hada hadadden website a kyauta sannan kuma ku samu kudi da website din, kusan yawancin webmaters da kuke gani yanzu sun fara ne da kananun webbuilder irinsu wapkiz,xtgem da wapka, mywapblog da dai sauransu kafin su koma blogger da WordPress

Ayanzu dai wapkiz shine best free webbuilder in the world duba da yadda yake da sabbabbin features kuma yake baiwa mutum daman saka tallan Adsense sabanin wasu webbulider din da vasa taba yadda a sanya tallan adsense a shafukan da aka kirkira da builder nasu.

Zamu fara darasinne akan yadda zaku hada Download website, wato shafin yanar gizo gizo da ake dora fayil fayil, irinsu wakoki,vidiyoyi,aplications da dai sauransu

Da fari kuje browser naku ku rubuta http://wapkiz.com zai kaiku shafin sai ku taba kan register dake a sama 


Daga nan zai kawoku wurin yin register din zakuga form sai ku cika da bayananku kaman 


Sai ku danna maballin Creat Now
Zai sake kawo ku wani wurin inda za a bukaci ku sanya sunan website din da kuke son budewa da short description nashi da kuma category na shafin, a wurin subdomain ku zabi wapkiz.com tayadda za arunga ziyartar shafinku kamar haka www.shafinku.wapkiz.com .

Kai tsaye bayan kun latsa maballin Creat Now zai kawoku panel na website naku inda a wurinne zaku fara designing website dinku, sai kuyi kasa kuje kan preset (template) 

Zai kawoku wurin template din sai ku zabi Download site tunda dama download site ne muke kokarin hadawa, Ku danna maballin Apply sannan Zai dawo daku shafinnaku inda zakuga shafin a ciki  design mai kyau


Sai ku tsumayemu a kashi na gaba wanda zamuyi bayanin yadda zaku dora wakoki da vidiyoyi da kuma yadda zaku bude category wa kowanne fayil

Wednesday, January 1, 2020

Kuna son sanin wake bibiyan (tracking) wayarku

Wayar Android wayace ta zamani data zo da abubuwan karuwa da dama, yawancin dalilan daya sanya mutane suke zaban wayar Android saboda features nata,  a dacan ana amfani da waya don kirane kawai (voice communication) ammafa yanzu an wuce babin don a yanzu wani ma in ka bincikeshi zaka samu badon kira bane ya siya wayarsa

Kusan duk wani abu da ake yi a computer na'ura mai kwakwalwa yanzu ana yinshi da wayar Android, kama daga kan design, editing da sauransu, 

Sai dai kuma da kwai wasu kwayoyin cuta dake bibiyan wayar Android wanda sun hada da malware,keylogers, trojans da sauransu wayanda suke lalata wayoyi, 

A irin wannan yanayi tabbatar da tsaron wayarmu itace abu mai muhimmanci, zamu lissafto wasu CODE wayanda zasu taimaka maku sosai wurin ganin SETTING na wayarku,  da sanar daku in wani na bibiyan kiranku, sako da sauransu

*#21#
Wannan code din zai taimaka maku wurin ganin ko ana bibiyan messages, calls da sauran data din wayarku, zaku iya samun bayanan call forwading naku, zaku iya ganin ko fax,sync,packet acces, sms, async da pad access call fowarding suna kunne ko suna kashe.

*#62#
Izan ana kiran nambarka yana nuna No service ko no Answer to ka dialing code dinnan a wayarka ta Android zai taimaka maka wurin sanin inane kiranka (calls) , messages da sauran abubuwan wayar suke tafiya izan an turo,  don kuwa ana iya hada redirected calls or messages, wato izan an kiraka maimakon kiran yazo layinka sai ya wuce layin wanda ke tracking naka,  ta hanyar amfani da code din can zaku iya gane hakan

*##002#
Wannan code din yana kulle gabadayan call forwading, kuma yana tsaida call or message redirection, izan kana fuskantar matsalar call redirection izan aka kiraka kiran na shiga wayar wani wannan na sauraran dukkan maganganun da kake a waya zaifi kyau kayi amfani da wannan code din kafin kayi roaming.


*#06#
Wannan code din da shine ganin (IMEI) International Mobile Equipment Identifier din waya, code dinnan yana da matukar amfani a babban waya, kasancewar yanzu koda an sata waya ana iya gano barawon wayar da taimakon IMEI

*##4636#*#* ko *#*#197328640#*#*
Wannan code din na musamman ne da taimakonshi wani zai iya bibiyan inda kake, sannan ya gane ko ana bibiyanka, misali izan barayi suka kidnapping wani to da taimakon wannan code din za'a iya gano inda wanda aka satan yake, har takai ga an kama barayin

GA YADDA ZAKU GANO INDA MUTUM YAKE

Ku dialing nambar ku shiga UMTS Cell Environment,  sannan ku shiga UMTS RR info. Daga nan sai ku kwashe nambobin dake karkashin cell ID.

Daga nan ku je MAIN MENU ku danna MM info ku zabi Serving PLMN. Sai ku kwashe nambobin dake karkashin Local Area Code (LAC)

Bayan kun kwafe nambobinnan sai ku je website din http://opencellid.org anan zaku iya binciken taswirar inda wayar keda hadaka da, kuma ku gano inda wannan mai wayar yake
Monday, December 30, 2019

Shin wayar ka/ki nayin slow da yawa ga yadda zaku magance marsalar
Assalamu'alaikum yau darasinmu zai tattauna ne akan yadda ake magance yawan slow din waya,

Izan wayarka ko wayarku na yawan yin slow wato tana jinkiri ga abubuwan da zakuyi kamar haka

Kada ku yarda kui amfani da BOOSTING APPS manhajoji masu kara wa waya sauri domin kuwa suna zuke cajin batiri

Izan kuna cikin amfani da application kuma kuna son fita kada ku fice ta hanyar goge manhajar,  ku danna madannin back har sai ya fitar daku daga applicatiob din hakan yana killace cajin batiri, 

Izan ya kasance baza kuyi amfani da wayar ba na dan lokaci sai ku sakata a cikin POWER SAVING MODE don killace cajin wayar

Ku unistalling komai da komai sannan ku kukkulle application na google da kukasan bakwa amfani da su irinsu, weather, google go,  da sauransu

Sannan kada ku yi amfani da application masu nauyi wayanda ba system app ba a cikin POWER SAVING MODE,don suna sanya waya tayi zafi da zuje cajin batiri,  iya application da zakui amfani da su sune wayanda sukazo da waya irinsu Setting, contact da sauransu

Sannan kada ku bari wayar ta dau zafi in ba haka ba kuwa, batirin wayar zai iya lalacewa, da zarar wayar ta day zafi ku kashe ta dan huta kafin sanda zatai sanyi


Kada ku yarda kuyi updating OS version na wayar, in ba dai kuna da matsala da existing one din bane duk da haka zai rage aikin wayar amman ku installing Security Updates,  wato tsohon hardware basa cika shiri da sabon OS, ta hakanne zakugan sun rufemaku wasu features din, sannan zakuna fuskantar wasu matsalolin, 

Amman dai kafin ku updating os din ku tabbata kun tuba reviews nashi kunga tsokacin jama'a akai

Bissalam
Daga Shuraih 99%

Sunday, December 29, 2019

Free browsing, kyautar data ga duk mai amfani da MTN da AIRTEL

Assalamu'alaikum

A yaune kamfanin opera suka sanar da zasu na bada kyautar data ga duk wani mai amfani da layin MTN ko AIRTEL, dun nuna farin cikinsu na shigar SABUWAR SHEKARAR 2020 NEW YEAR

Garabasar datan zai gudana ta cikin application nasu ne mai suna opera with free vpn.

Zaku iya shiga ko ina da datan sannan zaku iya dauko dukkan abunda kuke sa muradin daukowa amman ta cikin opera with free vpn.

Haryanzu dai basu sanar da ranar da zasu kulle garabasar ba

YADDA ZA'AI KU SAMU DATAN

Da farko ku dauko application din opera with free vpn Anan

DOWNLOAD OPERA WITH FREE VPN

Sannan ku tabbata simcard dinku MTN ne ko AIRTEL dun sune kawai suke da access da Opera

Bayan kun download sai ku bude ku cigaba da browsing kyauta, 
Sannan zaku iya bude application opera News  duka a kyauta, 

Wannan kyautar datan na opera sun kayyade shi izuwa 50 MB daily wato kullum kuna da daman ku sankami data 50 a kyauta, 

Kada kuyi wata wata abokai a kafta

Daga Shuraihu Usman
Inkiya 99%

Friday, December 27, 2019

Yadda zaku samu MB 600 a layin MTN kyauta
Assalamu'alaikum fatan kuna lafiya

Insha Allah yau darasinmu zai tattauna ne akan yadda zaku samu MB 500 ko 100 wasu ma zasu iya samun 600 a layin MTN ta hanyar amfani da MY MTN APP

Kusan kowa yasan manhajar (application) din MY MTN APP,  manhajar mymtnapp dai zai baka daman sayen data, sayen katin waya ta banki da sauransu,  sannan izan ya kasance baka taba amfani da manhajar ba da zarar ka bude zasu baka kyautar MB 500 

Yanzu kuma da kwai wata kyautar MB 100 da suke bayarwa a wannan watan,  wanda koda ace ka taba amfani da application din ko baka taba ba da zarar ka bude zasu baka zunzurutun MB har guda 100 

Izan kuwa baka taba budewa ba  yakasance wannan ne karon farkonka da budewa toh zasu baka MB 500 na budewar da kai sannan da MB 100 kyautar da suke bayarwa na wannan wata kaga izan ka hada ka samu MB 600 kenan 

YADDA ZAKA SAMU DATAN

 Da fari ka tabbata wayarka Android ce 
 Sannan sai ku downloading mymtnapp anan kasa

Bayan kun download na app din sai ku install sannan ku bude, zasu nemi ku sanya nambar wayarku bayan kun saka zasu turo da message mai dauke da  kalmar sirri na lokaci guda  (one time password) ta simcard din sai ku kwafe nambobin guda shida 6 ku dawo application din ku zuba take zasu bude application din.

In baku taba budewa ba a saman app din zaku ga ansaka 

YELLO! YOU HAVE BEEN REWARDED WITH 500 MB FREE DATA
Sai ku danna kan CLICK HERE TO ACTIVATE IT

Daga nan zasuyi maku message akan sun baku data 500mB kyauta sai ku danna *559*4# don duba data din izan kuka duba zakuga 600MB  harda kyautan da sukeyi

Izan kuwa ka taba budewa a saman zakaga an rubuta 

YOU HAVE BEEN REWARDED WITH 100 MB FREE DATA

sai ku danna kan CLICK HERE TO ACTIVATE IT atake zasu baku mb 100 sai ku danna *559*4# don duba MB din 

Duk Abunda baku gane ba ku yi tambaya a comment 

Dakwai wani darasinma na samun data 2GB a mtn kyauta kuma kullum

Wednesday, December 25, 2019

Abubuwan daya kamata mu kiyaye izan wayarmu tana cajiAssalamualaikum fatan Kuna cikin koshin lafiya a yau Kam zamuyi magana nee akan abubuwan Daya kamata mu kiyaye aikatawa izan wayarmu tana chaji

Dakwai wasu abubuwan da mukeyi izan muka sanya wayarmu a caji Wanda wannan Abu ba karamin hatsarine ga wayartamu da Kuma lafiyar mu ba
Wannan Abu kan janyo rashin karfin battery zuwa lalacewar waya da wuri hasalima zai iya janyo wa wayartamu tai bindiga Wanda hakan hatsarine ga lafiyarmu
Ga jerin abubuwan da bayanai akansu

YIN CHARGI DA KOWACCE IRIYAR CHARGER

Yin charging da kowacce iriyar charger hatsarine ga lafiyar wayarmu data batarinta, kusan yawanacinmu bamu damu da charji da kowacce iriyar charger ba mudai kawai muddin waya zatai chargi tofa babu ruwanmu da kalar charger din da muka sakamata Wanda hakan na ragewa batiri karfi, zaifi kyau mu nemi charger din wayar, izan ma zakai da kowacce iriyar charger to kafara duba (currentA) da mafitar Voltage (v) nata don sanin karfin charging charger din

AMFANI DA CHARGER MAI SAURIN CIKA WAYA

Maganar gaskiya anan shine babu Wanda ke chargi ya runga shigar wayarsa ahankali tamkar bazai shiga ba, to Amma inajin yafi kyau muyi hakuri don hausawa sunce Mai hakuri shike dafa dutse har yasha romonsa,

Kowa nason charger Mai CIKA way da wuri, Wanda izan ways tana 6% da kasa zuwa minti biyar zata koma 50% zancen gaskiya shine charger Mai CIKA way da wuri babu abunda take haifarma waya face ta lalata karfin battirin ka sabida ire iren chajar din suna daukene da voltage Mai karfi Wanda daga karshe zai Fara Santa wayarka tana daukar zafi,

So muddin Muna son wayarmu tai karko tofa dolenmu mu guji caji da chaja Mai cika ways cikin mintuna 30 ko 20 

YIN CAJI DA GIDAN WAYA (CONDOM) ko (CASE) a jikinsa

Gidan waya ba karamin kare wayoyinmu yake daga hatsari ba musamman ma faduwar waya a kas,
To Amma izan ya kasance zamu Sanya wayarmu a caji mukan manta da cireshi daga wayar Wanda hakan ba karamin hatsarine bane ga wayar tamu,
Domin kuwa dumin da ke jikin wayarmu bazai samu Daman fita cikin sauki ba sakamakon gidan wayar ya taresa, Wanda hakan zai it's janyo tarwatsewar wayar
Sai mu kiyaye Sanya gidan ways yayin chaji

KWANA ANA CAJI


Kusan dukkanmu Muna da wannan dabi'a ta barin ways ta KWANA tana caji, ba karamin abin Dadi bane ace ka kwanta wayarka na 0% ka farka ka sameta 100% Sai dai Kuma babban hatsarine ga lafiyar wayar don tana daukar zafi sosai inda Nan take karfin battirin ke raguwa 
Yana da kyau mu runga cire wayoyinmu a caji da zarar sun cika

YIN GAME KO FACEBOOK YAYIN CAJI

Wasu abun yabi musu jiki da zarar suna buga game ko Facebook caji ta kare tofa bazasu hakura ba Sai de su Sanya wayar a caji su cigaba da sha'aninsu
Hakan kuwa babbar hatsarine ga lafiyar su data wayar, domin hakan kan iya janyo wayar tayi dumi batiri ya lalace, kana Yana janyo waya taki yin caji da wuri

YIN CAJI DA SAURAN CAJI A WAYA

Wasu sunfi ganewa kowanne lokaci su runga Sanya wayar su a caji Sai kaga waya tana 70% ko 50% Amman sakata a caji, in laifin ma ka bari yakai 25%
Masana kimiyya sun sanar cewa yawan yiwa way caji na rage NAGARTA gamida karkon waya 

ANA CAJI DA POWER BANK KUMA ANA AMFANI DA WAYAR

Kusan abun ya rugaya ya zama ruwan dare a cikin mutane Ana caja waya da power bank kuma Ana amfani da wayar hakan kan janyo wayar ta yi dumi sosai inda inkai wasa ta rage Ma karfin batiri hakanan ya kan Sanya waya Bata karko take lalacewa da wuri
Mungode
Kuyi sharing sannan masu tambaya su ajjiyeta a comment
 

Tuesday, December 24, 2019

Yadda zaka bibiyi wayarka da aka sace ka gano inda take


Assalamualaikum fatan Kuna lafiya da yardar Allah yau zanyi maku bayani akan yadda Zaki bibiyi wayarku da aka sace har ku gano  barawon sa'annan ki gano wurinda wayar take,

A zamanin da izan aka sace maka waya tofa saidai Kai hakuri don kuwa inba sa'a kayi ba to har ka mutu bazaka sake ganin wayar taka, to Alhamdulillah yanzu ZAMANI tazo da fasaha ta yadda ake it's bibiyar wayar mutumin da aka sace Kuma a damki barawon

Kusan yanzu zakuga da an satarwa mutum ways Kai tsaye wurin hukuma yake nufa don bibiyi wayartasa inda hukuma zasu cajesa dubu goma Sha biyar, yayin da aka yi nasarar ganin wayar zasu maido masa da dubu goma Sha biyar dinsa da Kuma wayarsa Wanda kuma kudin zasu fito daga hannun Wanda aka Kama da wayarne,

To a irin yanayinnan zaka samu an satarwa mutum ways babba kirar Android Amma Kuma bayada dubu goma Sha biyar din da zaije a bibiyi wayar tasa (tracker), wasu ma izan suka biya kudin wa hukuma da zarar hukuma sun gagara Kama barawon gamida gano yanda wayar take tofa basa dawo masu da kudadensu kudin ya bi ruwa kenan

Izan ya kasance ka samu kanka a cikin Wayanda aka sacewa wa kirar Android ga matakan da zakabi na ganin wayarka ta dawo

Kai tsaye ka samu wata wayar ko ta abokinka koma na waye ka bude chrome ku rubuta www.google.com/android/find ko kuma ku dauko application din FIND MY DEVICE a playstore

Da kun shiga website sin sai ku saka Gmail address da kalmar sirri (password) naku dake jikin waccan wayar da aka sace maku,

Da zarar ya shigar da ku ciki zaku ga sunan waccan Wayartaku da aka sace a gefe guda sai ku latsa kansa sannan Google zai Fara binciken inda mazaunin wayar da aka satar take a wannan lokaci, baya daukan wani lokaci wurin you binciken yake iddarwa
Anan take zakuga wurin da wayarku take wato location, abun babu wahala

Amma kafin ku Fara bibiyar wayarku a yayin da kuja tabbatarda an satar maku waya, Kai tsaye ku Fara tuntubar bankinku day su kulle simcard din daga aiwatar da duk wani transaction, saboda ta hanyar simcard dinku za'a iya gano nambar BVN naku Kuma a ciri muku kudade ta bankinku Amma da zarar kun sanarwa da banking naku zasu dakatar da duk want transaction da nambar sannan su canza maku sabon namba

Fatan darasin namu zai taimaka sosai
Izan da Mai tambaya ya ajjiyeta a comment anan kasa