Monday, January 20, 2020

Garabasar katin waya na 100 daga kamfanin LaCaseraAssalamualaikum fatan kuna lafiya, bayan mun dan kwashe kankanin kwanaki baya babu post tom in Allah yayarda ayau muna dauke maku da yadda zaku samu kyautar 100 katin waya daga kamfanin lacasera.

Shin ko kunsan cewa a jikin kowanne goran lemun lacasera da kuke sha akwai kyautar katin waya na 100 wanda yake shiga kawanne irin layi kama daga kan,  MTN, AIRTEL, GLO, ETISALAT 


YADDA ZAKU SAMU KATIN WAYAN


Izan ku ka sayi Lacasera na 100 Naira sabon fitowa na wannan shekarar zaku gan goransa launin rawaya (yello)

Bayan kun shanye lemun sai ku duba murfin goran zaku ga wasu rubutu, ku kwafe rubutun ku turawa 20055 ta message.

Bayan kun tura zasu turo maku da wani sako sai ku zabi 1 zasu cire 10 naira a account naku.

Watom zasu ciri 10 naira su turomaka 100 naira ta layinka, kungan izan zaku sayi kati sai ku hutar da kanku, kawai ku sayi laCaseran 100 bayan kun zuka kuma ku samu kyautar 100 


Wednesday, January 15, 2020

Yadda zaku samu sama da 1GB data kyauta da kowanne layi
Assalam
Mun jima bamu kawo maku darasi akan data din kyauta ba tun bayan 150MB da aje samu kyauta da MTN,  ayau kam mun shirya tsaf don nuna maku yanda zaku samu data sama da 1GB a kowanne layi wato simcard

ABUBUWAN DA AKE BUKATA 

1. Wayar Android
2. Flaim apk
3. 2G network
4. Ilmi koyayane 

YADDA ZAKU SAMU DATAN

da fari ku tabbatar wayarku Android ce sai kuje playstored ku searchin flaim apk  ku download nashi ko kuma ku bi link dinnan download flaim

Bayan kun dauko apk din sai ku je ku maida network na wayanku zuwa 2G sannan ku dawi ku bude apk din ku latsa kan GETTING STARTED zaj kawoku inda zaku saka nambar wayarku, sai ku saka kudan jira kaman mintuna goma 10 zuwa goma sah biyar 15 zasu turo maku da confirmation code ta SMS sai ku kwafo code din ku dawo apk din ku zuba shi,

Kuna saka code din zakuga ya fara processing sai kuyi sauri ku danna back,  kada ku bari ya gama processing kuna dannawa za'a baku 75MB sai ku sake saka confirmation code din zai fara processing sai ku sake yin sauri ku taba maballin komawa baya (back button) na wayarku,  tun kafin ya bude maku paging gaba, a take zasu sake baku wani 75MB kunga in an hada da wancan an samu 150 MB sai ku cigaba da hakan zasu ta baku 75MB

Sai de fa datan yana tsawon kwanaki biyu ne kacal, 
Ku danna *131*4# dun duba data din

Monday, January 13, 2020

Garabasa daga kamfanin MTN, ku sayi 200MB da 50 naira
Assalamualaikum mabiya wannan shafi.
Kwanan Nan fa MTN Sai sakin Bonanza suke Yi ba kakkautawa, in Baku manta ba dakwai free browsing da akeyi kyauta da layin MTN, mun kawo maku darasin rannanYauwa Kuma bayan wayannan garabasa na data dakwai wasu na dabam wayanda muka kawosu sannan mukai bayaninsu anan haryanzu kuma suna amfani basuyi expire ba, 

To duk da haka mun cewa kwanakin baya mtn sun fidda wani tsarin sayen data mai suna INSTABINGE, wanda ake iya siyan datan 1GB akan 200, 250MB akan 100,  4GB akan 1000,  ga code din siyen datan *131*65# sai shi wannan tsarin na instabinge ba akowanne layi bane yakeyi

Kwatsam sai gashi mun discovering wata sabuwar hanya ta siyan 200MB akan 50 

Da fari ku danna *131*25* sai ku zabi 2, shikenan kun siya 200MB da 50 naira, 

Ammafa ku sani shima dai wannan tsarin kamar instabinge yake bakowanne layi bane keyi.

Friday, January 10, 2020

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!! sabon hanyar cutan da YAHOO BOYS suka fitar

Jama'a ku kiyaye kwanan nan 'yan yahoo boys sun fidda wata sabuwar hanyar cuta wadda suke kwasar wa mutum kudaden bankinsa da ita.

Da yawa daga cikinmu mun sani sukan kira mutum a waya su ce masa su ma'aikatan bankinsa ne sukan ce wai account naka ya samu matsala dun haka suna bukatan details din account dun su gyara maka,  waddda da zarar ka basu bayanan account naka tofa kai takare maka dun sun runga dibar kudaden account naka kenan har sai sun kare.

Tom yanzu sunga kusan kowa ya gano wancan hanyar da suke bi don cutan jama'a yanzu sunfiddo da sabuwar hanya wanda in baku kiyaye ba zaku iya ruftawa ciki, 

Sabon hanyar da suka fidda shi shine zakuga an turo maku da sakon EMAIL da sunan bankin da kuke amfani da shi akan an cire #2000 naira a cikin account din wai kudin subscription na bank magazines da ma wani bayanin da baka san da shi ba kuma baka nema ba, zasu cigaba da turo maku sakon email din duk karshen wata, wanda kaikuma ta ganin hakan hankalinka zai tashi ka fara tunanin yaushe kayi subscription na monthly magazine da har suke cire maka 2000 duk wata.

A karshen sakon Email din dakwai link din fita daga tsarin subscription din wanda in ka danna kan link din zai kaika wani shafi da zasu nemi ka saka bayanan bankinka kama daga kan account number, suna, banki, da BVN.

Muddin kuka yi gangancin cike wannan form din tofa naku yaja, dun a take zaku fara jin Alert ana zarar kudadenku babu dalili.

YADDA ZAKU KARE KANKU DAGA FADAWA KOMAR YAN YAHOO BOYS

Da zarar kunga sakon EMAIL makamancin wanda nai muku bayaninsa to ku rabu da email din, ko kuje banki ku duba account balance naku, kuga ko an taba,  inma an taba kuyi complain a cikin bankin.

Kada ku fara gangancin danna UNSUBSCRIBE daga link din sakon email din, ni in za kubi shawarata ma da zarar sun turo maku da irin sakon Email dinnan ku runga deleting nashi kawai, 

SHAWARA TA MUSAMMAN DON GUJEWA FADAWA KOMAR YAHOO BOYS

Zan baku shawara ta musamman wanda muddin kukai aiki da ita bana tunanin zaku fada komar 'yan yahoo boys.

Kufa sani duk yadda kuka kai ga wayo gamida taka tsantsan to mai son abunka yafika dabara, inji hausawa hakanan su yan yahoo boys dinnan wallahi basa da maraba da 'yan fashi.

Shawarar da zan baku shine ko waye kuma ko a ina ne,  kama daga kan Facebook, whatssap, instagram, twitter da sauran kafafen sada zumunta kada ku yadda ku baiwa wani bayanan bankinku,  kai koda ma ace ma'aikatan bankinne suke online kada ku basu,  face kunje branch na bankin, kai ko dama wasu kamfani ne suka bukaci ku basu bayanan bankinku kada ku basu,  domin kuwa Duniya ya lalace, mutumin Nigeria da kuke gani wallahi kuji tsoronsa kamar 💥 bomb,  

Inma account naku ya samu matsala kai tsaye sai ku wuce banki kuyi masu complain, 


WANNAN SANARWA NE DAGA JAMI'AN TSARON NIJERIYATuesday, January 7, 2020

Yadda zaku samu data 150MB a layin MTN ta hanyar Gidimo apk

Kwanakin baya wannan manhaja mai suna Gidimo suka fito inda suke baiwa duk wanda yai register da su data 150MB na MTN kuma ma register dasu kyauta ne in kuna da email an wuce wurin


ABUBUWAN DA AKE DA BUKATA

1. Email
2. Gidimo apk
3. MTN sim
4. Kankanin ilmi


Da fari ku fara dauko wannan manhajar ra gidimo a playstore 

Bayan kun dauko sai ku shiga ku danna SIGN UP zai kawoku wurin register, ku saka

Sunanku
Email dinku
Kalmar sirrinku (password)


Daga nan ku sai ku amince da dokokinsh ta hanyar ticking karamin akwatin kasannan sai ku danna kan SIGN UP shi kenan kunyi register sauran tabbatar da nanbar wayarku 

Kai tsaye nan zai kawoku sai ku taba kan Verify your phone number and get free 150MB 

Zasu kawoku wurinda zaku saka nambar wayar zasu turo verification code ta SMS sai minimixe ku duba inbox na messages naku zakuga sakon verification code din daga facebook sai ku kwashe code din ku dawo apk din ku zuba sannan ku danna verify a nan zasu verifying nambar sai kuyi back ku refreshing page din zasu nuna maku kun yi nasarar verifying nambarku don haka ku ajjiye nambarku su turo maku da 150MB Sai ku saka nambarku na MTN a wurin da suka bukaci ku saka nambar, sannan ku danna ok a take zasu turo maku da mb dari da hamsin kyauta, 

Aha duk wanda ke da tambaya ya yita a comnent

Sunday, January 5, 2020

Alamomin da zaku gane kasuwancin Bogi scam a internet
Kamar yadda na sha nanatawa, a intanet ana samun kudi sosai idan an yi da gaske. Wasu kuma suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna da wayon da suke yi su raba jama'a da abin hannunsu da sunan kasuwancin intanet. Masu irin wannan dabara suna da hanyoyi da yawa barkatai, har ma wani lokaci su ci da buguzum a dauka na gaskiya ne.

A yau na zakulo wasu daga hanyoyin da mutum zai yi wa kansa hukunci ya gane ko nau'in kasuwancin da aka bijiro masa na yi ne ko na bari. 
Ga su kamar haka:


1. Abubuwan da ake sayarwa: Idan ka ga yawancin kayan da ake sayarwa ba wasu fitattu ba ne, watakila ma ba wadanda ake iya gani ba ne. Wasu na kiransu 'Packages' ko 'Bundles' ko 'Subscription'. Yawanci babu wani abu a ciki sai zunzurutun shiririta. Da za a ce ka nuna abin da aka sayar maka ko irin aikinsa ba za ka iya ba.


2. Kankanin Kudi Babbar Riba: Daga yanayin ribar da aka yi alkawarin samu za ka fahimci akwai lauje cikin nadi. Duk wani kasuwancin intanet da yayi alƙawarin samun ninki biyu ko fiye na abin da ka zuba cikin wata daya, ka yi nesa - nesa da shi.


3. Shigo da wasu: Shi ne tsarin da ake kira 'Referral'. Watau za a ce idan ka kawo wani yayi rijista ta karkashinka za a baka wani abu na awalaja. Manyan kamfanoni fitattu kamar paypal da ebay da AliBaba da su Quickteller na nan Nijeriya duk suna yin haka, amma ba haka ta ci barkatai ba. Idan ka ga website na yin kasafin adadin kudin da za ka samu idan ka kawo mutane kaza zuwa kaza, lallai abin gudu ne.


4. Rijistar Kamfani: Kamar yadda muka san kamfanonin zahiri suna bukatar a yi musu rijista da hukuma, haka ma kamfanonin intanet. Kowanne kamfani akwai irin rijistar da ta kamace shi. A Nijeriya dai, bayan rijista da CAC, wajibi ne kamfani mai hada hadar kudi ya yi rijista da SEC matukar yana da mutane 50 ko fiye da suka zuba kudinsu a cikinsa komai kankantar kudin.


5. Shugabanni da Jagororin kamfani: Idan ka ga kamfani ya boye sunayen shugabanninsa an rumbun bayanai na Whois, to ka guje shi. Daga nan ne ake gane inda aka dosa har a iya tofa albarkacin baki. Kodayake, wasu na yin dabara su rubuta bayanan bogi a cikin rumbun. Don haka sai an kula kafin a saki jiki da su.


6. Takardun Shaida: A Nijeriya, wajibi ne ga kamfani ya karbi wasu takardun bayanai daga masu son zuba hannun jari a cikinsa. Takardun shaidar sun hada da katin shaida, hoton mutum da BVN da katin dan kasa da kuma takardar biyan kudin ruwa ko wuta ko wata takardar shaida da ke nuna adireshin mutum. Watau irin takardun da ake bude asusun banki da su. Duk kamfanin da ka ga ya kasance daga buhu sai tukunya, watau daga ka yi rijista da su ka zuba kudi sai kurum ka saurari 'alert', to abin gudu ne.


7. Ka'idojin Rubutu: Yawancin kamfanonin kasuwancin bogi ba su damu da rubutu cikin ingantattun hanyoyin ka'idojin rubutu ba. A kowane yare suke rubutun za ka ga kura-kurai barkatai tare da saka kalmomin da basu dace ba. Illar haka shi ne rasa martaba a farfajiyar duniyar google ta fuskar SEO. Wannan su ba damuwar su ba ne, saboda masu taya su tallan kamfanin suna iya isar da sakon da ake bukata ta kafafen soshiyal midiya.


Ba duka aka taru aka zama daya ba, ko anan Nijeriya akwai kasuwancin intanet mai riba sosai wanda ba gara ba zago. Ni ma na zuba a wasu daga cikinsu. Wadannan kamfanoni sun hada da I-Invest, Payday, Elixir, AlatNg da sauransu. Kowacce rana hukumar SEC tana bibiyar ayyukan wadannan kamfanonin, ta yadda koda sun durkushe mutum zai iya maida asarar da ya yi.

Daga Danladi Z Haruna

Friday, January 3, 2020

Yadda zaku samu datan glo mara iyaka a kyauta
Wannan datar da ake samu shine mutane da dama ke siyar maku da tsananin tsada wanda inajin kwana biyu
Kenan da fitowar data din, 

Amman kar ku damu nauyinmu ne mu nuna maku yadda zaku samu wannan data din a kyauta maimakon ku siya a wurin wasu.

ABUBUWAN DA AKE BUKATA

1. Layin Glo guda biyu
2. Katin Glo na 200 naira
3. Waya kirar Android ko OIS
4. Service 3G ko 4G
5. Tsarin Glo yakata *230#

YADDA ZAKU DATAN

Yana da matukar muhimmanci izan kun samu datannan kuyi amfani da shi da wuri,  kunga dai ba kowa ke bada shi a kyauta ba sai an biya to yanzu da muka fara nuna wa a kyauta ba wuya ya barbazu a duniya har suji su kulle, sannan kuyi amfani da datar wurin dauko abubuwa masu ma'ana gamida amfani

Ku samu datan Glo guda biyu na farkon dole ya kasance yana tsarin Glo yakata  ne ku danna *239# don shiga tsarin

Daga nan sai ku loda katin 200 ko sama da hakan amman kar yayi kasa da 200 sannan ku subscribtion din data na 200 ( glo yakata suna bada 250mb ne sabanin 50mb )

Bayan awanni biyu 2 250mb din zai zo layinku, daga nan sai ku sharing mb din zuwa dayan layin glo dinku ta hanyar amfani da wayannan nambobi *127*01* ku saka nambar waccan sim din anan#

Anan take Zaku samu mb mara karewa wato unlimited a dayan layin wanda duk abun da zakuyi ba zai taba karewa ba, tofa amma abokai kunsan subscribtion din kunyi na awanni 24 ne bayan awannanin subs din zai kare mb din zai tsaya, in kuna son ku more datan sosai kuyi subsdin wata guda ne kunga zakuci bulus har tsawon wata guda kenan

Yadda zaku hada (simple download website) a wapkiz kashi na daya 1
Assalamu'alaikum da yardan Allah yau zamu fara darasi akan yadda zaku gina website naku na kanku a shafin gina website (webbuilder) na wapkiz.

Wapkiz dai webbuilder ne da zai baku daman hada hadadden website a kyauta sannan kuma ku samu kudi da website din, kusan yawancin webmaters da kuke gani yanzu sun fara ne da kananun webbuilder irinsu wapkiz,xtgem da wapka, mywapblog da dai sauransu kafin su koma blogger da WordPress

Ayanzu dai wapkiz shine best free webbuilder in the world duba da yadda yake da sabbabbin features kuma yake baiwa mutum daman saka tallan Adsense sabanin wasu webbulider din da vasa taba yadda a sanya tallan adsense a shafukan da aka kirkira da builder nasu.

Zamu fara darasinne akan yadda zaku hada Download website, wato shafin yanar gizo gizo da ake dora fayil fayil, irinsu wakoki,vidiyoyi,aplications da dai sauransu

Da fari kuje browser naku ku rubuta http://wapkiz.com zai kaiku shafin sai ku taba kan register dake a sama 


Daga nan zai kawoku wurin yin register din zakuga form sai ku cika da bayananku kaman 


Sai ku danna maballin Creat Now
Zai sake kawo ku wani wurin inda za a bukaci ku sanya sunan website din da kuke son budewa da short description nashi da kuma category na shafin, a wurin subdomain ku zabi wapkiz.com tayadda za arunga ziyartar shafinku kamar haka www.shafinku.wapkiz.com .

Kai tsaye bayan kun latsa maballin Creat Now zai kawoku panel na website naku inda a wurinne zaku fara designing website dinku, sai kuyi kasa kuje kan preset (template) 

Zai kawoku wurin template din sai ku zabi Download site tunda dama download site ne muke kokarin hadawa, Ku danna maballin Apply sannan Zai dawo daku shafinnaku inda zakuga shafin a ciki  design mai kyau


Sai ku tsumayemu a kashi na gaba wanda zamuyi bayanin yadda zaku dora wakoki da vidiyoyi da kuma yadda zaku bude category wa kowanne fayil

Wednesday, January 1, 2020

Kuna son sanin wake bibiyan (tracking) wayarku

Wayar Android wayace ta zamani data zo da abubuwan karuwa da dama, yawancin dalilan daya sanya mutane suke zaban wayar Android saboda features nata,  a dacan ana amfani da waya don kirane kawai (voice communication) ammafa yanzu an wuce babin don a yanzu wani ma in ka bincikeshi zaka samu badon kira bane ya siya wayarsa

Kusan duk wani abu da ake yi a computer na'ura mai kwakwalwa yanzu ana yinshi da wayar Android, kama daga kan design, editing da sauransu, 

Sai dai kuma da kwai wasu kwayoyin cuta dake bibiyan wayar Android wanda sun hada da malware,keylogers, trojans da sauransu wayanda suke lalata wayoyi, 

A irin wannan yanayi tabbatar da tsaron wayarmu itace abu mai muhimmanci, zamu lissafto wasu CODE wayanda zasu taimaka maku sosai wurin ganin SETTING na wayarku,  da sanar daku in wani na bibiyan kiranku, sako da sauransu

*#21#
Wannan code din zai taimaka maku wurin ganin ko ana bibiyan messages, calls da sauran data din wayarku, zaku iya samun bayanan call forwading naku, zaku iya ganin ko fax,sync,packet acces, sms, async da pad access call fowarding suna kunne ko suna kashe.

*#62#
Izan ana kiran nambarka yana nuna No service ko no Answer to ka dialing code dinnan a wayarka ta Android zai taimaka maka wurin sanin inane kiranka (calls) , messages da sauran abubuwan wayar suke tafiya izan an turo,  don kuwa ana iya hada redirected calls or messages, wato izan an kiraka maimakon kiran yazo layinka sai ya wuce layin wanda ke tracking naka,  ta hanyar amfani da code din can zaku iya gane hakan

*##002#
Wannan code din yana kulle gabadayan call forwading, kuma yana tsaida call or message redirection, izan kana fuskantar matsalar call redirection izan aka kiraka kiran na shiga wayar wani wannan na sauraran dukkan maganganun da kake a waya zaifi kyau kayi amfani da wannan code din kafin kayi roaming.


*#06#
Wannan code din da shine ganin (IMEI) International Mobile Equipment Identifier din waya, code dinnan yana da matukar amfani a babban waya, kasancewar yanzu koda an sata waya ana iya gano barawon wayar da taimakon IMEI

*##4636#*#* ko *#*#197328640#*#*
Wannan code din na musamman ne da taimakonshi wani zai iya bibiyan inda kake, sannan ya gane ko ana bibiyanka, misali izan barayi suka kidnapping wani to da taimakon wannan code din za'a iya gano inda wanda aka satan yake, har takai ga an kama barayin

GA YADDA ZAKU GANO INDA MUTUM YAKE

Ku dialing nambar ku shiga UMTS Cell Environment,  sannan ku shiga UMTS RR info. Daga nan sai ku kwashe nambobin dake karkashin cell ID.

Daga nan ku je MAIN MENU ku danna MM info ku zabi Serving PLMN. Sai ku kwashe nambobin dake karkashin Local Area Code (LAC)

Bayan kun kwafe nambobinnan sai ku je website din http://opencellid.org anan zaku iya binciken taswirar inda wayar keda hadaka da, kuma ku gano inda wannan mai wayar yake
Monday, December 30, 2019

Shin wayar ka/ki nayin slow da yawa ga yadda zaku magance marsalar
Assalamu'alaikum yau darasinmu zai tattauna ne akan yadda ake magance yawan slow din waya,

Izan wayarka ko wayarku na yawan yin slow wato tana jinkiri ga abubuwan da zakuyi kamar haka

Kada ku yarda kui amfani da BOOSTING APPS manhajoji masu kara wa waya sauri domin kuwa suna zuke cajin batiri

Izan kuna cikin amfani da application kuma kuna son fita kada ku fice ta hanyar goge manhajar,  ku danna madannin back har sai ya fitar daku daga applicatiob din hakan yana killace cajin batiri, 

Izan ya kasance baza kuyi amfani da wayar ba na dan lokaci sai ku sakata a cikin POWER SAVING MODE don killace cajin wayar

Ku unistalling komai da komai sannan ku kukkulle application na google da kukasan bakwa amfani da su irinsu, weather, google go,  da sauransu

Sannan kada ku yi amfani da application masu nauyi wayanda ba system app ba a cikin POWER SAVING MODE,don suna sanya waya tayi zafi da zuje cajin batiri,  iya application da zakui amfani da su sune wayanda sukazo da waya irinsu Setting, contact da sauransu

Sannan kada ku bari wayar ta dau zafi in ba haka ba kuwa, batirin wayar zai iya lalacewa, da zarar wayar ta day zafi ku kashe ta dan huta kafin sanda zatai sanyi


Kada ku yarda kuyi updating OS version na wayar, in ba dai kuna da matsala da existing one din bane duk da haka zai rage aikin wayar amman ku installing Security Updates,  wato tsohon hardware basa cika shiri da sabon OS, ta hakanne zakugan sun rufemaku wasu features din, sannan zakuna fuskantar wasu matsalolin, 

Amman dai kafin ku updating os din ku tabbata kun tuba reviews nashi kunga tsokacin jama'a akai

Bissalam
Daga Shuraih 99%